1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon abinci ga kasar Nijer

August 12, 2005

Sako-Sako da aka yi a game da barazanar barnar farin dango shi ne musabbabin hali na kaka-nika-yi da kasar Nijer ta samu kanta a ciki yanzu haka

https://p.dw.com/p/BvaT

A dai halin da ake ciki yanzu matakan taimakon abincin ga kasar Nijer sun kankama ko da yake har yau da sauran rina a kaba dangane da kokarin da ake yi na shawo kann bala’in yunwar da ya rutsa da kasar ta yammacin Afurka. Ita ma kungiyar taimako ta Red Cross, reshen Jamus, ta gabatar da matakan taimako na gaggawa tare da jigilar kayan taimako zuwa kasar nijer. A lokacin wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Berlin yau juma’a, wakilinta akan al’amuran Afurka Dietrich Fischer yayi nuni da cewar an shirya jigilar kayan taimako ta sama har sau biyar zuwa kasar ta Nijer, inda a kowace tafiya za a kai taimakon abincin da yawansa ya kama tan 60. Fischer sai ya kara da cewar:

Kayan taimakon sun hada da man girki da wake da shinkafa da sinadaren gina jiki ga yara masu fama da karancin abinci mai gina jiki, sai kuma magunguna, musamman na riga-kafin billar cutar kwalera, saboda wannan cuta tuni ta zama kayar kifi a wuya. A baya ga haka an tanadi kunshe-kunshe na kayan girki saboda rabawa tsakanin mutanen da tuni suka kama hanyarsu ta yin kaura daga yankunan da bala’in yunwar ya rutsa dasu.

To sai dai kuma wannan taimakon daga Jamus bai taka kara ya karya ba, idan aka ba da la’akari da mawuyacin halin da kasar Nijer ta samu kanta a cikin yanzu haka. Bugu da kari kuma kungiyoyin taimako masu zaman kansu kamar Red Cross, wadanda suka dogara kacokam akan gudummawa daga jama’a, jigilar kayan taimakon ta sama abu ne dake musu tsada matuka ainun. Kawo yanzu duka-duka taimakon da aka tara daga jama’a bai zarce Euro dubu 400 ba, a yayinda gwamnati tayi alkawarin ba da gudummawar Euro dubu 800. Amma fa a halin yanzu haka kungiyar Red Cross na kula ne da makomar mutane kimanin dubu 500 a yankunan Tawa da Maradi da Zinder. Musabbabin wannan mawuyacin halin da Nijer ta samu kanta a ciki shi ne ko oho da duniya tayi da gargadin da kwararrun masana suka gabatar a game da barazanar fuskantar barna daga farin dango dake lalata amfanin noma a cikin kiftawa da Bisimillah. Ana iya kawar da kwayayen farin ta amfani da magungunan kashe kwari, amma sai aka rika sako-sako wajen ba da taimakon kudin da ya cancanta domin tinkarar matsalar tun daga tushenta. A baya ga haka an fuskanci mummunar matsalar fari a yankin Sahel hade da tabarbarewar al’amuran siyasa. Muhimmin abin da ake bukata a wannan yanki shi ne nagartattun hanyoyin noman rani da kayyade yawan haifuwa da kyautata ilimi da kuma amfanin noma mai karko da kuma bunkasa a cikin gaggawa. Amma taimakon abinci na gajeren lokaci kawai ba zai wadatar ba.