1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon KTT Ga Palasdinawa

November 10, 2004

Ana zargin shugaban Palasdinawa Malam Yassir Arafat da wawashe kudaden taimakon raya yankunan Palasdinawa abin da ya saka shi a cikon na shida daga cikin jerin sarakuna da shuagabannin da suka fi kudi a duniya

https://p.dw.com/p/Bvem
Arafat da Mahmoud Abbas
Arafat da Mahmoud AbbasHoto: AP

An dai kiyasce cewar shugaban na Palasdinawa Malam Yassir Arafat ya tara abin da ya kai dalar Amurka miliyan 300 ko da yake hukumar leken asirin Isra’ila na batu a game da sdala miliyan 700 da ya tara su bai daya, domin dogara akansu idan har kasar Isra’ilar ta tilasta masa zaman hijira a ketare. A halin yanzu haka an shiga tafka mahawara a Brussels a game da rawar da Kungiyar Tarayyar Turai ke takawa a game da kudaden ajiyar na Arafat a matsayinta na cibiyar ba da taimako mafi tsoka ga Palasdinawa. An dai dade ana rade-radi a game da kudaden da Malam Yassir Arafat ya tara a asurce a bankunan kasashen ketare, kuma asusun ba da lamuni na duniya IMF shi ne ya fara billo da wannan maganar a shekarar da ta wuce, inda yake batu a game da wasu kudade na dalar Amurka miliyan 900 da ba wanda ya san makomarsu. Abin da ake tababa akansa dai shi ne, yawan kudaden taimako nawa ne suka mula, kuma wannan maganar ta fi shafar KTT saboda ita ce akan gaba wajen ba da taimako ga Palasdinawa domin giggina makarantu da asibitoci da kuma ayyukan noma. Amma fa ba a koda-yaushe ne kungiyar ke bin diddigin makomar wadannan kudade na taimako ba, ko Ya-Allah an aiwatar da su akan ainifin shirye-shiryen da aka tanada. A lokacin da yake bayani Armin Laschet, wakilin CDU a majalisar Turai cewa yayi:

A tsakanin shekara ta 2002 zuwa shekara ta 2003 KTT kan tura abin da ya kai Euro miliyan 10 domin cike gibin kasafin kudin Palasdinawa a kowane wata ba tare da shimfida wani sharadi ba. Hakan ta haifar da korafi a tsakanin wakilan majalisar Turai, inda aka dakatar da wannan manufa aka mayar da hankali zuwa ga taimakon shirye-shiryen raya yankunan Palasdinawan dake da ikon cin gashin kansu. A saboda haka a yanzun akwai cikakkiyar masaniya a game da inda kudaden ke kwarara.

To sai dai kuma duk da haka ita hukumar zartaswa ta KTT mai sa baki wajen gabatar da kudaden taimakon ta shiga wani hali na tsaka mai wuya. A bangare guda dai ana da labarin yaduwar cin hanci da son kai tsakanin mahukuntan Palasdinawa, amma a daya bangaren babbar manufar da aka sa gaba ita ce ta rufa wa yankunan Palasdinawan masu ikon cin gashin kansu baya da kuma sassauta radadin talaucin dake addabar mazauna yankunan. To amma tun abin da ya kama daga farkon wannan shekarar mahukunta a Brussels suka fara bin bahasi akan zargin da ake wa Malam Arafat da mukarrabansa a game da watandaran da kudaden taimakon daga KTT. Muhimmin abu a yanzun, kamar yadda Armin Laschet ya nunar shi ne kungiyar ta fito fili ta bayyanar cewar ta gabatar da taimakon ne domin amfanin al’umar Palasdinawa, amma ba saboda arzuta mahukuntan Palasdinu ba. Kazalika wajibi ne kungiyar ta dora hannu akan kudaden ajiyar dake bankunanta da kuma bankunan kasar switzerland tun kafin su sulale zuwa aljifun uwargidan Malam Arafat ko wani daga cikin dangi ko mukarrabansa.