1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon mutunen da ta'addanci ya shafa

Gazali Abdou Tasawa
January 9, 2017

Kasar Faransa ta bayyana bukatar ganin kasashen duniya sun kaddamar da wani shiri na musamman na taimaka wa mutanen da harin ta'addanci ya rutsa da su a daidai lokacin da hare haren ta'addanci ke kara yaduwa a duniya. 

https://p.dw.com/p/2VXNC
Israel LKW-Anschlag in Jerusalem
Hoto: Reuters/R. Zvulun


Kasar Faransa ta bayyana bukatar ganin kasashen duniya sun kaddamar da wani shiri na musamman na taimaka wa mutanen da harin ta'addanci ya rutsa da su a daidai lokacin da hare haren ta'addanci ke kara yaduwa a duniya. Minista kana sakatariyar kula da ayyukan jin kai ta kasar Faransa Juliette Méadel  ta gabatar da wannan shawara a taron kasa da kasa kan batun tallafa wa mutanen da harin ta'addanci ya ritsa da su da aka bude a wannan Litinin a birnin Paris wanda kasashe kimanin 20 ke halarta. Ministan ta kara da cewa matsalolin ta'addanci da bukatar tallafa wa mutanen da lamarin ya rutsa da su , mataki ne dake bukatar taron dangi. Matakin na bukatar a cewar ministan kaddamar da nan zuwa shekara ta 2027 da wata siyasar bay daya kan batutuwa hudu da suka hada da masayar bayanai kan mutanen da ta'addanci ya ritsa da iyalansu, da daukar mauyin 'yan kasashen waje da lamarin ya ritsa da su, basu tallafi da daukar nauyin kula da lafiyarsu cikin sauri da kuma biyansu kudin diyya.