1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon raya kasashe masu tasowa

August 23, 2005

Kwararrun masana masu tarin yawa na gabatar da kiran dakatar da manufofin taimakon raya kasashe masu tasowa saboda taimakon baya tsinana musu kome

https://p.dw.com/p/BvaI

A cikin wata hira da mujallar Der Spiegel tayi da shi, wani kwararren masanin al’amuran tattalin arziki dan kasar Kenya mai suna James Shikawati ya bayyana cewar manufofin taimakon raya kasa na taimakawa wajen dasa kasala da kiwa a zukatan al’umar afurka tare da mayar da su tamkar masu yawon da kokon bara don neman taimako. Kazalika ana amfani da wadannan kudade wajen karfafa manufofi na dogon turanci da rufa wa cin hanci baya. A misalin shekaru biyar da suka wuce Jamus ta dakatar da taimakon da take ba wa kasar Cap Verdes, ita ma kungiyar Tarayyar Turai ta bijire wa kasar Togo tun misalin shekaru 10 da suka wuce, a yayinda makobciyarta Benin ke samun taimakon Euro miliyan 300 a shekara sakamakon manufofinta na demokradiyya. Amma fa duk da haka akwai gibin kasashe 15 tsakanin Togo da Benin dangane da wadatar arziki, bisa tsarin MDD. Sannan ita kuma Cap Verdes ba wani banbancin da aka samu a game da halin da kasar take ciki misalin shekaru ashirin da suka wuce da kuma shekaru biyar na dakatar da taimakon Jamus ga kasar ta yammacin Afurka. Kazalika an yi shekaru masu yawa kasashe kamar Mali da Nijer na cin gajiyar taimakon raya kasa daga kasar Jamus. Amma fa wannan taimako ba wani abin a zo a gani da ya tsinana wa wadannan kasashe. Kusan mutane miliyan biyu ke fama da matsalar yunwa a kasar Nijer sakamakon rashin damina mai albarka da kuma bala’in farin dango wadanda suka bannatar da amfanin da ta noma. Yawa-yawancin alumar Nijer da Mali na zama ne hannu baka hannu kwarya a yayinda kashi daya bisa uku daga cikinsu ke fama da karancin abinci mai gina jiki. To ko shin ana iya cewar manufofin taimakon raya kasashe masu tasowan ba su da wani alfanu? Bisa ga ra’ayin Michael Lossner, darektan ofishin kungiyar taimakon fasaha ta Jamus GTZ a kasar Nijer, inda ya kara da cewar:

A cikin shekaru 17 da suka wuce mun samu kafar farfado da yanayin kasar yankin Tillebery dake kusa da Yammai, inda ake da ikon noma fili mai fadin eka dubu 400 yanzu haka. Wannan fili a zamanin baya ya zama fako ba a iya noma a cikinsa sakamakon rashin bin wata kyakkyawar hanya ta tattali da tanadin yankin.

Amma fa duk da haka akwai masu adawa da manufofin na raya kasa, abun da ya hada har da wasu daga cikin ma’aikatan taimakon, wadanda galibi ba sa son a ambaci sunayensu saboda gudun asarar guraben ayyukansu. Dalinsu dai shi ne na cewar ‚yan boko ko kuma ‚yan gata, wadanda suka hada da jami’an siyasa da mahukunta, sune ainifin matsalar dake addabar Afurka. Domin kusan babu wata kasa ta Afurka da ba ta fama da matsalar cin hanci da rashawa. Babban misali a nan shi ne gwamnatin kasar Libiya ta ba wa Nijer taimakon dubban tan na dabino sakamakon bala’in yunwar da ya rutsa da ita. Shi kuwa gwamnan lardin Agadez da ya karbi wannan taimako sai ya raba wa abokai da mukarrabansa, domin sayarwa ga mayunwatan a kasuwa.