1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon soja daga NATO da EU ga Darfur

June 9, 2005

Kungiyoyin NATO da EU sun cimma daidaituwa wajen raba nauyin taimakon Darfur daidai wa daida tsakaninsu

https://p.dw.com/p/BvbQ

Amurka, wacce ta kwatanta tashe-tashen hankulan lardin Darfur a matsayin wani mataki na kisan kare-dangi tare da kiran mayar da martani ba da wata-wata ba, ta bukaci ganin kungiyar tsaron ta NATO ta dauki nauysin jigilar dukkan sojojin baki dayansu. Amma a sakamakon adawar da aka fuskanta daga kasar Faransa bisa dalilin kasancewar tuni KTT ta shiga dumu-dumu ana damawa da ita a fafutukar neman zaman lafiyar lardin na Darfur, sai aka cimma daidaituwa akan raba nauyin jigilar sojojin su kimanin dubu biyar, a tsakanin kungiyoyin guda biyu, wato ta NATO da ta tarayyar Turai. An saurara daga bakin sakatare-janar na kungiyar NATO Jaap de Hoop Scheffer yana mai yin nuni da cewar al’amura sun dada rincabewa a lardin ta yadda ya zama wajibi dukkan kungiyoyin guda biyu su yi aiki kafada-da-kafada wajen shawo kann lamarin, kuma wajibi ne a fara da kungiyar tarayyar Turai, wacce tuntuni dake ba wa kungiyar tarayyar Afurka goyan baya a kokarinta na samar da zaman lafiyar lardin Darfur. Wani jami’in kungiyar ta NATO ya musunta rahotannin dake nuna cewar an samu sabani mai tsananin gaske tsakanin NATO da EU akan wannan batu. Ya ce irin wannan sabani da ake batu ba zai tsinana kome ba illa ya kawo tafiyar hawainiya, inda za a bata wasu makonni biyu ko uku ana kokarin dinke barakar a maimakon mayar da hankali akan ainifin manufar da aka sa gaba. A lokacin taronsu da ya kai har tsakar daren jiya laraba ministocin tsaron kasashen kungiyar NATO sun cimma daidaituwa akan ba wa kowace kasa dake da wakilci a cikin kungiyoyin guda biyu cikakkiyar dama ta zabar bangaren da take sha’awar shiga a dama da ita a matakin na taimakon soja. Kasashen Jamus da Faransa da Italiya zasu ba da gudummawarsu ce ta kann kungiyar tarayyar Turai EU, a yayinda ita kuma Amurka zata gabatar da taimakonta karkashin tutar kungiyar NATO. Ana sa ran ministocin tsaron zasu albarkaci yarjejeniyar kana daga baya su tattauna a game da ainifin gundarin matakan taimakon, wanda a baya ga jigilar soja ya kuma tanadi ba da horo ga sojojin kiyaye zaman lafiyar na kasashen Afurka. Ita dai Amurka, kamar yadda ake kyautata zato zata yi amfani da filayen jiragen saman Nijeriya da Ruwanda ne wajen kwashe sojojin zuwa Darfur, a yayinda Faransa zata rika jigilar sojojin daga Senegal. Kawo yanzu ba a cimma daidaituwa ba a game da bangaren da zai rika debo sojojin daga ATK zuwa Darfur. Kazalika babu wata takamaimiyar ranar da aka tsayar domin fara wannan hidima ko da yake kungiyar tarayyar Afurka ta bayyana fatanta game da gabatar da matakin daga watan yuli mai zuwa.