1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan zaben kananan hukumomi a Nijar

February 13, 2017

A Jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyi masu fafatukar kare demokradiya sun tayar wa gwamnati kayar baya da nufin tilasta mata shirya zabukan kananan hukumomi.

https://p.dw.com/p/2XUfB
Niger Hamdoullaye Wählerinnen
Hoto: DW/M. Kanta

Alhaji Nouhou Arzika daya daga cikin 'yan gwagwarmaya masu fafatukar kare hakin demukradiyya ya bayyana bacin ransa dangance da batun dage zabukan mashawartan kananan hukumomi biyo bayan kawowa dab da karshen wa’adin shugabanninsu da gwamnatin ta bayar a baya bisa wasu dalilai da ta kira na rashin tsabtataccen kundin rijistar sunayen masu zabe na ainihi da take son amfani da shi.

Kungiyoyin na fararen hular dai na yunkurin tilasta wa gwamnati don karkato mata akala domin ganin ko ta halin kaka ta shirya zabukan na kananan hukumomi wanda 'yan rajin kare hakin na demukradiyya ke yi wa ikirari da cewar shi ne kadai zaben da ke a matsayin ginshikin tafiyar demukradiyya tun daga tushe. Saboda haka rashin shirya zaben tamkar wani karan tsaye ne ga demukradiyyar. Alhaji Nouhou Arzika jagoran hadin gwiwar kungiyoyin Mouvement citoyen ya ce:

''Mutane ne da ake son su ci gaba da iko ba tare da yardar al’umma alhali kuwa babu wata yarda ta al’umma kuma duk ko ina ana kuka da su babu amana da yardar al’umma, kenan wajibi ne yau a bai wa al’umma damar daukar duk wadanda za su wakilce su tare da sake sabon zaben wakilan, wanda ya yi abin kirki ya ci gaba, wanda bai yi ba kuma su kore shi amma haka kawai sai a ce mike. Ai abin kunya ne ga wadanda suka ce sun yi kokuwar tazarce a ce a lokacinsu ne aka yi ta-mike cikin dubara.''

A ka’idance a ranar 16 ga wannan watan ne ya kamata a ce wa’adin shugabannin na kananan hukumomi da ma majalisun jihohi ya kawo karshe bisa wani karin wa’adin da gwamnatin ta yi masu a can baya wanda kuma tun kafin hakan ya kamata a ce shugaban kasa ya kira wata yekuwar zabe don maye gurbinsu tun a cikin watan Oktoban shekarar bara.  
Sai dai wani taron gungun 'yan siyasa a karkashin hukumar CNDP ya bai wa gwamnati shawarar gudanar da zaben bisa dalilan abubuwan da 'yan farar hular suka ce ba za ta sabu ba. Malam Sidi Fodi Hamissou kusa ne a kungiyoyin CODDAE:

Yadda jami'an zabe a Nijar ke gudanar da aikin kidayar kuri'u a zabukan baya
Yadda jami'an zabe a Nijar ke gudanar da aikin kidayar kuri'u a zabukan bayaHoto: DW/A. Amadou

''Idan ba’a yi zaben nan ba to lallai kam demukradiyya an takata kuma demukradiyya bata da lafiya saboda lafiyar demukradiyya zaben nan na karkara, wadannan magadan gari da ba sa aikin komai.


Sai dai a wata fira da tashar DW ministan cikin gida Malam Bazoum Mohamed ya ce matakin shawarar da 'yan siyasar suka bai wa gwamnati abin dubawa ne duba da tsare-tsaren da gwamnatin kasar take son bullowa da shi game da kundin rijistar sunayen masu zabe, kana daga yanzu za ta ci gaba da ba wa shugabannin kananan hukumomin karin wa’adi har izuwa tsawon wa’adin da gwamnatin take da hurumin yin zaben.

A ranar 16 ga wannan watan ne wa’adin na biyu da gwamnati ta bai wa hukumomin zai kare inda ake sa ran ta sake daukar wani mataki tare da ci gaba da yin hakan har tsawon shekaru matsayin bai wuce wa’adin mulki na shekaru biyar ba a cewar wata sabuwar doka da majalisar dokokin kasar ta amince da kungiyoyin fararen hula suka ce za su kalubalanta jini da fata.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani