1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama tsakanin Sudan da MDD

April 5, 2006

MDD tayi Allah waddai da matakin gwamnatin Sudan na hana wakilinta Jan Egeland kai ziyara Darfur

https://p.dw.com/p/Bu0o
Jan Egeland
Jan EgelandHoto: AP

A lokacin da take hira da manema labarai, wakiliyar Amurka a MDD Jakie Sanders ta ce wajibi ne kasar Sudan ta ba da hadin kai musamman a fannin taimakon jinkai, amma fadar mulki ta Khartoum na ko oho da lamarin. Sanders ta ce ta nemi kwamitin sulhu na MDD da yayi kakkausan suka tare da Allah waddai da matakin da gwamnatin Sudan ta dauka na kin ba wa Jan Egeland, wakilin majalisar akan matakan taimakon jinkai damar kai ziyara lardin Darfur domin ya gane wa idanuwansa mawuyacin halin da jama’a ke ciki. A baya ga haka kasar ta Sudan ta hana wa jirgin dake dauke da Jan Egeland ratsawa ta samaniyarta domin kai ziyara makobciyar kasa ta Chadi. Rahotanni masu nasaba da majiyoyi na diplomasiyya sun ce kasashen Rasha da China da kuma Katar, su ne suka ki amincewa da ta shawarar ta yi wa fadar mulki ta Khartoum tofin Allah tsine, sai dai kawai a mayar da hankali akan mawuyacin halin da ake ciki a lardin Darfur.

A nasa bangaren Jan egeland ya fada wa manema labarai cewar matakin da gwamnatin Sudan ta dauka na haramta masa kai ziyara lardin Darfur na mai yin nuni ne da yadda al’amura ke dada tabarbarewa a wannan lardi da kuma dusashewar dangantaka tsakanin MDD da fadar mulki ta Khartoum sakamakon sabanin da ake yi game da mayar da ayyukan kiyaye zaman lafiyar Darfur karkashin tutar MDD. A dai halin da ake ciki yanzu kungiyar tarayyar Afurka ce ke tafiyar da matakan kiyaye zaman lafiyar tare da dakarunta su dubu bakwai, wadanda aka ce ba su da ikon ba da cikakkiyar kariya ga mazauna yankunan karkara na wannan lardi daga hare-haren dakarun sa kai na larabawa, wadanda ke samun goyan baya daga fadar mulki ta Khartoum. A baya ga haka su kansu dakarun kiyaye zaman lafiyar na Kungiyar tarayyar Afurka ana zarginsu da laifuka na fyade da cin zarafin kananan yara a yankin Gereida dake karkashin ikon ‘yan tawaye, wadanda suka shiga takun-saka da sojojin na kungiyar AU saboda dagewar da suka yi na cewar lalle sai an mayar da Gereida wani yanki na ‘yan ba ruwana.

A cikin wata sabuwa kuma wani rahoton da aka bayar dangane da mutuwar tsofon mataimakin shugaban kasar Sudan John Garang ya dora laifin faduwar jirgin sama mai saukar ungulu dake dauke da shi akan matukin jirgin. Hatsarin ya afku ne lokacin da Garang ke kan hanyarsa ta ziyarar abokinsa Yoweri Museveni, amma da yawa daga ‘yan kudancin Sudan sun shiga zanga-zangar da yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 100 a birnin Khartoum bisa zargin cewar wannan mutuwa ta fuj’a da Garang yayi wata makarkashiya ce ta kisan kai aka shirya masa.