1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar dake akwai a game da taron Annapolis

Ibrahim SaniNovember 28, 2007
https://p.dw.com/p/CUDf

Shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad ya ce kwalliya ba za ta biyu kuɗin sabulu ba, a game da taron da aka kammala na Yankin Gabas ta Tsakiya a birnin Annapolis. Ahmadinejad ya ci gaba da cewa, Amirka ta shirya taron ne kawai, a matsayin farfaganda. Buƙatar Amirka game da taron a cewar shugaban na Iran ita ce na inganta tare da faɗaɗa matsayin Israela, a yankin na Gabas ta Tsakiya. Shugaba Bush, wanda ya ɗauki nauyin taron na Annapolis, ya ce za a ci gaba da tuntuɓar juna har sai kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Taron wuni ɗayan na Annapolis ya cimma ƙudirin samar da ´Yantacciyar ƙasar Falasɗinu, tare da warware rikicin dake tsakanin Israela da Falasɗinawa.