1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar shirin nukiliyar Iran ta ta´azzara

January 14, 2006
https://p.dw.com/p/BvCH

Iran ta ce ba zata yi sassauci ba a shirinta na nukiliya da ake takaddama akai ko da an yi karar ta a gaban kwamtin sulhu na MDD. Shugaba Mahmud Ahmedi-Nijad ya fadawa wani taron manema labarai a birnin Teheran cewa kasarsa zata kare ´yancin ta na mallakar fasahar nukiliya kuma ta na da tanade tanade bisa wannan manufa. Shugaba Ahmedi-Nijad ya ce Iran ba zata mika kai ga matsin lambar kasashen yamma ba. A kuma halin da ake ciki sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleeza Rice ta tuntubi takwarar aikinta na China Li Zahoxing inda suka tattauna game da yiwuwar tura wannan batu a gaban kwamitin sulhu. A ranar litinin mai zuwa jami´an kasashen tarayyar Turai da na Amirka da China da kuma Rasha zasu gudanar da shawarwari a birnin London, inda ake sa rai zasu sanya ranar da za´a gudanar da taron gaggawa na hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa.