1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar Turkiya da Tarayyar Turai EU

Lateefa Mustapha Ja'afarAugust 1, 2016

Turkiya ta ce za ta yi watsi da yarjejeniyar 'yan gudun hijira da ta cimma da kungiyar EU in har ba su amince da bai wa 'yan kasarta damar shiga kasashensu ba tare da Visa ba.

https://p.dw.com/p/1JZp7
Wakilan Turkiya da EU yayin cimma yarjejeniya kan 'yan gudun hijira
Wakilan Turkiya da EU yayin cimma yarjejeniya kan 'yan gudun hijiraHoto: picture alliance/dpa/L.Du Brule

Ministan harkokin kasashen ketare na Turkiya Mevlüt Cavusoglu ne ya ambata hakan, sai dai a hannu guda kungiyar ta EU ta yi gargadin cewa ya zamo wajibi Turkiya ta cika dukkan sharuddan samun wannan izinin da ma na yarjejeniyarsu kan batun 'yan gudun hijrar kafin 'yan kasarta su samu damar shige da fice a kasashen na EU ba tare da takardar Visa ba. Da yake zantawa da manema labarai kan wannan batu, ministan tattalin arziki da makamashi na Jamus Sigmar Gabriel cewa ya yi:

"Babu wani abu da zai sauya dangane da bai wa 'yan Turkiya damar shiga Turai ba tare da takardar izini na "Visa" ba, Turkiya za ta ci wannan gajiyar ne kawai in ta cimma ka'idojin kungiyar EU. Wannan ya rage ga Turkiya, ba za mu amince ta fake da batun damar shiga kasashen EU ba tare da Visa ba domin cimma wata manufarta ta daban. Kasar da ta dawo da batun hukunci kisa a kasarta, ta cirewa kanta wasu damarmaki na shiga cikin sahun kasashen Turai."