1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaita zurga-zurgar jirage a Heathrow

August 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bumr

Hukumar filin jirgin saman Heathrow na London ya yi barazanar daukar matakai na haramta saukar jirage masu jigilar fasinjoji idan kamfanonin hada hadar jiragen saman basu rage yawan jirage masu jigilar sauka a filin jirgin na Heathrow ba. A wata sanarwa da shugaban filin jirgin saman na Heathrow Tony Douglas ya aikewa kamfanonin jiragen fasinja, wadanda ke da jirage dake sauka sau uku ko fiye da haka a filin na Heathrow a kowace rana su gabatar masa da sabon jadawali na tsarin hada hadar jiragen tare da takaita zurga zurgar jiragen da kimanin kashi 30 cikin dari. Jamiín ya yi barazanar hanawa kamfanonin jiragen da suka yi burus da wannan umarni muhimman bukatu na saukar jiragen. Kamfanin British Airways ya sanar da soke kashi 20 ciki dari na zurga zurgar jiragen sa daga yau Litinin bisa bin umarnin hukumar jiragen saman na Britaniya tare kuma da soke tashin jirage 26 wadanda ke zurga zurga na cikin gida daga filin jirgin sama na Gatwick.