1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaitaccen Tarihin Gestine Schwan 'Yar Takarar SPD A Zaben Shugaban Kasar Jamus

May 19, 2004

A ranar lahadi 23 ga wata ne za a zabi sabon shugaban kasar Jamus, wanda zai maye gurbin shugaba mai barin gado Johannes Rau. Kuma ko da yake an hakikance cewar dan takarar CDU/CSU da FDP Horst Köhler, shi ne zai lashe zaben sakamakon rinjayen da jam'iyyun ke da shi a majalisar tarayya, amma 'yar takarar SPD Farfesa Gestine Schwan ba ta fid da kauna a game da cimma nasarar zaben ba

https://p.dw.com/p/BvjR
Gestine Schwan 'yar takarar SPD a zaben shugaban kasar Jamus
Gestine Schwan 'yar takarar SPD a zaben shugaban kasar JamusHoto: dpa

Gestine Schwan ‚yar takarar SPD da The Greens, babbar malamar siyasa dake da shekaru 60 da haifuwa, sau dari hudu tana bayyana a bainar jama’a tun abin da ya kama daga farkon watan maris da ya wuce. Ta kewaya duk fadin kasar a matakinta da za a iya kwatanta shi da wata manufa ta yakin neman zabe. Kuma ko da yake babu wani mai tababa a game da nasarar dan takarar ‚yan Christian Union da FDP Horst Köhler, amma Gestine Schwan ta sikankance cewar tana da wata ‚yar dama ta tsallake rijiya da baya. A lokacin da take bayani jami’ar, babbar masaniya akan al’amuran siyasa ta ce ita kam a rayuwarta ta fi kaunar tinkarar matsaloli masu sarkakiyar gaske, wadanda sai an sha fama da yarfe gumi wajen neman bakin zaren warwaresu, wadannan matsaloli sune suka fi burge ta. Wani abin sha’awa, in ji ta, shi ne kowa-da-kowa ya hakikance da mutumin da zai lashe zaben, kuma a saboda haka sai ta ci karenta babu babbaka, ba wani abin da zai canza dangane da lamarin. Amma fa wannan ba shi ne ra’ayinta ba. Muhimmin abin da ta sa gaba a yanzun shi ne sake janyo hankalin Jamusawa zuwa ga siyasar kasarsu, bayan fatali da suka yi da ita sakamakon gundura da karerayin ‚yan siyasa.

Ga alamu dai wannan jami’ar in har ta cimma nasara ba zata zauna ta harde kafafuwanta akan kujerar mulki ba. Domin kuwa Gesine Schwan mace ce mai kazar-kazar kuma ba ta ganin zarau sai ta tsinka. An sha fama da sabani tsakaninta da jam’iyyarta ta SPD. Misali a cikin shekarun 1970 tayi bakin jini tsakanin masu ra’ayin gurguzu na jam’iyyar SPD abin da ya hada har da shugaban gwamnati Gerhard Schröder sakamakon goyan bayan da ta ba wa wani kuduri mai fuskoki biyu da kungiyar tsaro ta NATO ta gabatar. Hakan da sanya aka kakkabeta daga wakilcinta a kwamitin kula da shikashikan manufofin jam’iyyar ta SPD a shekarar 1984. Tun abin da ya kama daga shekarar 1999 farfesa Schwan take shugabancin jami'ar Turai ta Viadrina dake garin Frankfurt Oder a gabacin Jamus. Bisa ga ra’ayinta dai, kasancewarta mace, shi ne ainifin dalilin da ya sanya shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya tsayar da ita domin takarar neman zama shugaban kasar Jamus, saboda a matsayinta na ‚yan mace zata ba wa wannan mukami wani sabon jini. Gesine Schwan na da ‚ya’yan biyu, kuma mijinta ya rasu a shekarar 1989. Abokin tarayyarta a yanzun shi ne Peter Eigen tsofon shugaban bankin duniya, kuma darektan kungiyar yakin da cin hanci ta kasa da kasa, Transparency International, a halin yanzu. A ranar asabar mai zuwa, a jajibirin zaben na shugaban kasa, farfesa Gesine Schwan zata yi bikin samun shekaru 61 da haifuwa.