1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaitaccen tarihin irin al'adun da 'yan Afirka sukayi tarayya a ciki

October 27, 2009

Ko akwai wasu al'adu iri guda da ƙabilun afirka daban daban ke dasu?

https://p.dw.com/p/KGLK
Gidan wasa na farko a AfirkaHoto: DW-TV

Afirka - nahiya ce mai faɗin gaske, wadda ke da al'adun da jama'ar yankin, suka gada kaka - da - kakanni. Suna kuma bin addinai da yanayin rayuwar da za'a iya gani a harkokinsu na yau da kullum, kama daga yanayin bauta da cin abinci da kuma yanda suke yin bukukuwa da dai sauransu.

Ana samun banbanci a yanayin al'adar al'ummar Afirka ne saboda faɗin yankunan da suke zaune, inda ake samun waɗanda ke rayuwa a wuraren dake da dausayi, tsaunuka, ƙoramu da dai sauransu. Saboda haka, abune mai wuya mutum ya yi magana akan al'adar jama'ar nahiyar. Wasu daga cikin 'Yan Afirka, sukan yi aure fiye da guda, a yayin da wasu kuma, ke yin aure guda ɗaya tak. Wasu na danganta kansu ne da ɓangaren Uwa, a yayin da wasu kuma ke ɗaukar ɓangaren Uba.

Bildergalerie Africa Festival 2009
Bukin gargajiyaHoto: Horst A. Friedrichs

Hakanan, Manoma, da Makiyaya, da kuma masu bayar da maganin gargajiya - misali, suna da irin al'adar da suka yi tarayya a ciki - kowannensu, kamar kuma yanda a yanzu, al'adun al'ummomin nahiyar Asiya, ko kuma Turai suka yi ta'asiri - ya zuwa wani matsayi a cikin al'adar mutanen Afirka, ko dai saboda addini ko kuma saboda zaman tare na tsawon lokaci. Sai dai kuma, duk da haka wani abu guda da al'ummomin Afirka suka yi tarayya akai, shi ne bayar da fifiko ga batun Iyali ko kuma Dangi, musamman a wajen gudanar da bukin aure, binne gawa, da sauran bukukuwa.

Idan muka ɗauki bukin aure - alal misali, ƙabilun Afirka da dama suna mutunta irin tufafin da za'a sanya, da waƙe - waƙen da za'a yi da kuma raye - raye a matsayin rukunan bukukuwan. Kazalika galibin ƙabilun Afirka, suna ƙarfafawa matasa gwiwar yin aure da sauri - musamman da zarar sun fara balaga. Sukan kuma himmatu wajen tattaunawa tsakanin Iyalan ɓangaren miji da mata, domin sulhunta aure a duk lokacin da aka samu saɓani tsakanin ma'aurata.

Bdt Bulgarien Pferd bei Rennen in der Nähe von Sofia
Hoto: AP

Al'ummomin nahiyar afirka na bin addinai daban daban da suka haɗa dana Musulunci da Kiristanci, kana wasu na bin addinin gargajiya. Sai dai kuma mafi rinjayen ƙabilun Afirka sun yi imani da cewar, Allah maɗaukakin Sarki ɗaya ne. Hakanan da dama daga cikin ƙabilun na afirka, sun yi amanna da masu bada magungunan gargajiya, kamar yanda wasu kuma suka yi imani da bokaye a matsayin waɗanda zasu shige musu gaba wajen neman biyan buƙata daga Mahalicci.

Sai kuma tambayar da ta fito daga hannun Malama Falmata Bukar daga Maiduguri a jihar Bornon tarayyar Najeriya. Malama Falmata ta ce, yau she ake sa rai da daren lailatul kadri, kuma shin dagaske ne a daren Lailatul Kadri ana ganin komai yana yin sujada, kamar bishiyoyi da gidaje, kuma mutum yana iya hango ka'aba daga duk inda yake?

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Zainab Mohammed