1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaitaccen Tarihin Sabon Shugaban Kasar Jamus

June 30, 2004

A gobe alhamis ne za a yi bikin nadin sabon shugaban kasar Jamus Horst Köhler, wanda yayi kimanin shekaru hudu a mukamin darektan asusun ba da lamuni na IMF a birnin Washington

https://p.dw.com/p/BviX
Horst Köhler sabon shugaban kasar Jamus
Horst Köhler sabon shugaban kasar JamusHoto: dpa

Horst Köhler dake da shekaru 61 da haifuwa, kwararren masani ne akan al’amuran kudi da tattalin arziki, wanda ya taba zama karamin minista a ofishin shugaban gwamnati Helmut Kohl kafin a nada shi darektan asusun ba da lamuni na IMF dake birnin Washington. Ba tare da wata rufa-rufa ba ya fito fili ya ce ba ya da wata masaniya a game da takamaiman yanayin siyasar Jamus da alakar rukunonin siyasarta. Horst Köhler dai, ana iya cewar, ya shiga siyasar ne da rana tsaka, saboda ba ya faro ne daga tushe tun daga reshen matasa na wata jam’iyya ta siyasa zuwa ga kananan hukuma da majalisar jiha har ya zuwa majalisar dokoki ta Bundestag kamar yadda lamarin yake dangane da sauran jami’an siyasa a nan Jamus. Amma fa sabon shugaban zai iya cike wannan gibi da ficen da yayi a dangantaku na kasa da kasa. Kai tsaye bayan zabarsa da aka yi domin takarar neman mukamin na shugaban kasa, an saurara daga Horst Köhler yana mai bayanin cewar:

A sakamakon aikina na tsawon shekaru hudu a Washington da kuma wasu shekaru biyu a bankin rayawa na kasashen Turai a birnin London, na samun ikon saduwa da cude-ni-in-cuzde-ka da jinsunan mutane masu al’adu da addinai iri dabam-dabam daga kusan dukkan sassa na duniya. Hakan ta taimaka wajen kyautata alakata da kowa-da-kowa.

A shekarar 1943 aka haifi Horst Köhler a yankin Skierbieszow na kasar Poland. A shekarar 1953 iyayensa suka karaso zuwa garin Ludwigsburg a kusa da Stuttgart. Bayan da ya kammala sakandare Köhler ya karanta kimiyyar tattalin arziki a jami’ar Tübingen, inda ya ci gaba da aiki a cibiyar binciken tattalin arziki ta jami’ar. A shekarar 1976 ya koma ma’aikatar tattalin arzikin Jamus sannan a 1981 ya amsa kiran da tsofon gwamnan jihar Schleswig-Holstein Gerhard Stoltenberg yayi masa domin rike mukamin maga-takarda a ofishin gwamnan. Ba’ada bayan haka an nada shi karamin minista a ma’aikatar shugaban gwamnati Helmut Kohl a shekarar 1990. Sannan a 1993 ya kama aiki a matsayin shugaban gamayyar bankunan ajiya na Jamus, kafin a nada shi darektan asusun ba da lamuni na IMF a Washington a shekarar 1998. A lokacin da aka tambaye shi dalilin da ya sanya ya sauka daga wannan mukami domin amsa kiran da aka yi masa na tsayawa takarar shugaban kasa Köhler cewa yayi a takaice, saboda kishin kasarsa. Ya ce wajibi ne ya bauta wa kasar saboda ta bude masa hanyoyin cimma nasarori dabam-dabam a rayuwarsa. Ba kuwa yi wata-wata ba wajen bayyana goyan bayansa ga kundin nan na garambawul da gwamnati ta gabatar karkashin taken "Agenda 2010", wanda ya ce abu ne dake da muhimmanci matuka ainun dangane da makomar kasar ta Jamus baki daya.