1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaitaccen tarihin Yahya Jammeh Shugaban kasar Gambiya

Salissou BoukariMarch 16, 2016

Yaushe ne shugaba Yahya Jammeh ya fara mulki a kasar Gambiya, sannan wai shi soja ne ko kuma farar hula ne, kuma wace kasa ta yi wa Gambiya mulkin mallaka.

https://p.dw.com/p/1IEE7
Yahya Jammeh
Alhaji Yahya Jammeh Shugaban kasar GambiyaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Shi dai Yahya Jammeh an haifeshi ne a ranar 25 ga watan Mayu na 1965 a garin Kanilai na kasar ta Gambiya, kuma iyayansa talakawa ne. Sannan Yahya Jammeh soja ne, domin ya yi wata makarantar aikin soja ta kasar Amirka da ake kira (Ecole des Amériques pour la Coopération de sécurité, ko (Western Hemisphere Institute for Security Cooperation). Makaranta ce da ke horas da sojoji daga kasashe dabam-dabam na duniya a cikin yanayi na huldar harkokin tsaro tsakanin kasar Amirka da sauran kasashe. Sannan tarihi ya nunar cewa da dama daga cikin wadanda suka samu horo a wannan makaranta ta soja, sun kwaci mulki ta hanyar juyin mulki a kasashensu.

Yahya Jammeh
Alhadji Yahya Jammeh Shugaban kasar Gambiya da masu tsaron lafiyarsaHoto: AP

Shi ma dai Yahya Jammeh yana da mukamin Laftanan na soja ne ya jagoranci wani juyin mulki wanda ya bashi damar darewa kan karagar mulkin kasar a ranar 22 ga watan Yuli na 1994 bayan da ya kifar da gwamnatin Shugaba Dawda Jawara wanda ke mulkin kasar tun daga samun mulkin kai har ya zuwa wannan lokaci da aka kifar da shi.

Shugaba Yahaya Jammeh ya ajiye kayan soja inda ya koma ga tsari na farar hula na siyasa, abun da ya kai shi ga kafa wata jam'iyya mai suna APRC (Alliance Patriotique pour la Reorientation et la Construction) da ke a matsayin wata jam'iyya da za ta dukufa wajan kawo sauyi da gina kasa, wadda tun wannan lokaci take jagorancin kasar ta Gambiya.

Shugaba Yahya Jammeh ya shirya zaben shugaban kasa na farko a ranar 29 ga watan Satumba na 1996 wanda ya bashi damar zaman shugaban Jamhuriyar Gambiya duk kuwa da cewa zaben da aka yi na cike da konkonto dangane da sahihancinsa.

An sake zabensa a wani sabon wa'adin mulki na biyu a ranar 18 ga watan Oktoba na 2001 inda ya lashe zaben tun a zagayen farko da kashi 53 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada.

Al Hadji Yahya Jammeh
Alhadji Yahya Jammeh Shugaban kasar GambiyaHoto: AP

Ba tare da wasu wahalhalu ba kuma shugaba Jammeh ya sake samun wani sabon wa'adi na uku inda ya sake lashe zaben kasar a ranar 22 ga watan Satumba na 2006 a wannan karo da kashi 67.33 cikin 100 yayin da abokin hamayyarsa lawya kuma dan rajin kare hakin dan Adam Ousainou Darboe ya samu kashi 26.6 cikin 100. Zaben da a wannan lokaci kungiyar tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ta CEDEAO ko ECOWAS ta ce an yi zaben na gaskiya, sai dai shugaban yayi amfani da kayayakin da suka fuce kima wajan yakin neman zabe a gaban abokin hamayyarsa.

A ranar 24 ga watan Nuwamba na 2011 an sake zaben shugaba Yahya Jammeh a wani sabon wa'adin mulki na hudu na tsawon shekaru biyar, inda ya samu lashe zaben da kashi 71.6 cikin 100 yayin da abokin hamayyar ta shi na kullun Ousainou Darboe ya samu kashi 17.4 cikin 100, sai dan takara na uku Hamat Bah shi kuma ya samu sama da kashi 11cikin 100.

To a watan Maris na 2014 Shugaba Jammeh ya canza harshen da kasar ke amfani da shi a hakumance inda daga turancin Ingilishi suka koma Larabci, abun da masu sharhi a lokacin ke kallo a matsayin wani yunkuri na karfafa dangantaka da kasashen Larabawa, tare da neman mayar da kasar kan ta farki na shari'ar Muslunci.

A ranar 30 ga watan Disamba na 2014, yayin da yake cikin wani bulaguro a kasashen waje, wani tsofon Captain din soja mai suna Lamine Sanneh ya jogorancin yunkurin kifar da gwamnatin ta Yahya jammeh sai dai bai samu nasara ba. Sai a ranar 12 ga watan Disamba na 2015 Shugaban kasar ta Gambiya ya ayyana kasar a matsayin Jamhuriyar Muslunci.

Batun kare hakin dan Adam a kasar ta Gambiya

Kasashen da dama dai na yi wa shugaban na Gambiya kallon wanda ya ke aiwatar da kama karya a kasarsa, inda a ranar 28 ga watan Satumba na 2009 yayin wata hira da aka yi da shi ta gidan talbijin na kasar, Yahya Jammeh ya yi barazanar hallaka 'yan rajin kare hakin dan Adam na kasar inda yake zarginsu da neman tadda zaune tsaye a cikin kasa. Sannan kuma a ranar 02 ga watan Oktoba na 2013 shugaba Jammeh ya sanar da fitar kasarsa daga kungiyar Commonwealth ta kasashen renon Burtaniya a wani mataki na nuna kin amincewarsa da katsalandan da suka ce kasar da ta renesu ta Britaniya na yi musu a fannin kare hakin dan Adam.

Batun incin kafofin yada labarai a Gambiya

Kungiyar 'yan jaridu na duniya Reporters sans frontières, ta ayyana shugaban na Gambiya Yahya Jammeh a matsayin babban mai take hakin fadar albarkacin baki na 'yan jaridu, inda a shekarun 2004 da 2005 ya amince da wasu dokoki biyu da ke kayyade incin fadar albarkacin baki na 'yan jaridu a kasar, sannan da kisan gilla da aka yi wa wani dan jarida mai suna Deyda Hydara wani mai adawa da manufofin shugaban kasar. baya ba da kame-kamen da hukumar jami'an tsaro na farin kaya ta kasar ta Gambiya NIA ta yi wa 'yan jaridu a kasar, tare da saka su a gidan kaso.

Sani a fannin magunguna na gargajiya?

Kamar yadda ake fada, shugaban na Gambiya na da matukar sani a fannin magungunan gargajiya, inda ma a shekarar 2007 ya sanar cewa yana iya warkas da cutar SIDA da Asma ta hanyar magungunnan gargajiya. Sannan a ranar 20 ga watan Augusta na wannan shekara Shugaba Jammeh ya sanar cewa da ya hada wani magani ta hanyar itatuwa da ke iya warkas da cutar hawan jini, inda da dama daga cikin ministocinsa suka shaida cewa sun samu waraka ta hanyar magungunan da ya hada na gargajiya.