1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takarar Buhari 2019 ta ja hankalin Jaridu

Abdullahi Tanko Bala
April 13, 2018

Sanarwar da shugaban Najeriya Muhammadu ya yi cewa zai sake tsayawa takarar zabe a 2019 ya dauki hankali a ciki da wajen Najeriya, har ma ya dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/2w20o
Karikatur: Buhari Candidacy
Hoto: DW

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce ziyarar da shugaba Buhari ya kai zuwa Lagos ya sami tagomashi na dumbin jama’a da suka yi dafifi domin yi masa maraba a cewar jaridar, ko da yake shugaba Buhari ya sha alwashin bunkasa tattalin arzikin kasar a lokacin yakin neman zabe a 2015, to amma ga bangaren 'yan adawa sun nuna cewa har yanzu basu gani a kasa ba.

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgameine Zeitung, ta duba batun sace wani Bajamushe ne a Jamhuriyar Nijar. Jaridar ta ce Bajamushen wanda ma'aikaci ne na taimakon raya kasa, shi da direbansa, ba su iya tsira daga mahara ba. Maharan wadanda ke kan babura su hudu dauke da makamai, sun tsayar da direban motar, inda nan take suka yi awon gaba da Bajamushen da direban nasa wanda dan kasar Nijar zuwa cikin sahara tsakanin Mali da Nijar.

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi nata sharhin ne akan batun tsare wasu limamai 30 wadanda ake tuhuma da yada ta'addanci a kasar Senegal. A shari'ar da aka fara yi wa mutanen, an tuhumesu da tallafawa masu aikata ta'addanci. Jaridar ta ce a ranar Litinin din makon wannan kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 15 a gidan kaso da kuma yin aiki tilas ga daya daga cikin mutanen da ake tuhuma mai suna Ibrahima Ly wanda ke da takardun zama dan kasar Senegal da Faransa. An dai kama shi ne a kasar Faransa, inda kuma aka tabbatar da cewa ya halarci sansanin kungiyar IS a kasar Siriya.

Batun gurbacewar muhalli shi ne ya dauki hankalin Jaridar Neues Deutschland, wadda ta leka kasar Mozambik. Jaridar ta ruwaito cewa tun lokacin da aka gano iskar gas a gabar ruwan kasar kasar ta Mozambik, kamfanin Shell mai hakar mai tare da sauran kafanonin hakar man suka dukufa aiki don tuno arzikin da ke shimfide a karkashin kasar. Jaridar ta kara da cewa komai na da tasa illar, domin yayinda ake murnar cewa matalauciyar kasar da ke gabashin Afirka ta samu hanyar samun kudin shiga, a waje daya kuma gurbacewar muhalli a yankunan da ake hakar man yana neman kawo cikas ga rayuwar al'umma.

A sharhinta Jaridar Der Spiegel ta yi tsokaci ne kan mutuwar Winnie Mandela, tsohuwar yar gwagwamrmayan yaki da wariyar launin fata. Jaridar ta ce Winnie Madikizela-Mandela ta tafi ta bar tarihi, ba kawai ga 'yan jam'iyar ANC da sauran 'yan Afirka ta kudu kadai ba, labarinta ya watsu a duniya bisa jajircewar da ta yi lokacin da tsohon mijinta marigayi Nelson Mandela ke daure a gidan yari. Ko da yake daga baya an zarge ta da wata tabargaza da ta danganci kisa.