1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takarar mata a zaben Cote d'Ivoire

December 16, 2016

A wannan karo mata da dama ne suka tsaya takarar neman kujerar 'yan majalisa a kasar Cote d'Ivoire a wani mataki na neman taka rawa sosai a fagen siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/2UNpW
Elfenbeinküste Referendum Wahl Abidjan
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Mata kimanin 200 ne kotun tsarin mulkin kasar Cote d'Ivoire ta amince da takararsu daga cikin mata 344 da suka aje takardun neman tsayawar takarar neman kujerar dan majalisar a zaben na wannan karo. Da take tsokaci kan takarar matan Rachele Gogoua shugaban kawancan kungiyoyin matan kasar ta Cote d'Ivoire ta gargadi matan kasar da su tsaya takarar 'yan majalisa a wannan karo, bayyana lamarin ta yi da cewa wani babban abun ci gaba ne. Yasmina Ouegnin wata 'yan majalisar dokoki a kasar ta Cote d'Ivoire da ta sake tsayawa takara a wannan zaben, ta yi kira ga mata da su tashi su nemi ko wani rin mukami na shugabanci domin a cewarta ita kanta ba ta yi kasa  a gwiwa ba a cikin aikinta na 'yar majalisa.

Elfenbeinküste Wahl und Unruhen Flash-Galerie
Hoto: AP

Mazaje musamman 'yan siyasa da dama ne a kasar ta Cote d'Ivoire suka soma tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan yunkuri da matan kasar ke yi a zaben 'yan majalisar na wannan karo. Bertin N'Dri tsohon dan majalisa ne amma a zaben shekara ta 2011 ya ki tsayawa takarar domin bai wa wata mata damar hawa kujerarsa a majalisa. Kuma yana mai ra'ayin cewa matan na da 'yancin hawa ko wane mukami musamman idan an dage ga basu damar samun ilimi. Wannan ce ma ta kai shi ga bude wasu cibiyoyi na bai wa matan horo irin na yaki da jahilci tare da shirya wasu daga cikinsu domin tsayawa takara a wannan zabe ya na mai cewa:

Ya ce: "A batun zaben 'yan majalisa ko wani zabe na daban, ba wai dan mace na mace ne ba zai sa jama'a su zabe ta ba, ya danganci yadda suke kallon matsayin mata da ko sun amince su wakilce su a majalisa. Amma a zahiri take lamurra na sauyawa kamar yadda muka gani mace ta kai ga samun shugabanci a Laberiya mai makoftaka da tamu kasar. Dan haka muna kyautata fatan ganin an kai ga samun irin wanann canji a nan Cote d'Ivoire. Ina fatan kafin Allah ya dauki raina ya nuna mani ranar da mace za ta samu shugabanci kasa a kasarmu ta Cote d'Ivoire."

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani