1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Take-taken shugaba Bush game da 'yan jarida

April 20, 2004

A sakamakon wahalar da ya kan sha fama da ita wajen amsa tambayoyi masu sarkakiya daga 'yan jarida shugaba George W. Bush na Amurka ya kan yi bakin kokarinsa wajen kauce wa tarurruka tare da manema labarai

https://p.dw.com/p/BvkS
Shugaba Bush lokacin wani taron manema labarai a makon jiya
Shugaba Bush lokacin wani taron manema labarai a makon jiyaHoto: AP

Jami’ai a fadar mulki ta White House su kan shiga kaka-nika-yi a duk lokacin da aka shirya wani taron manema labarai da zai dauki lokaci mai tsawo tare da shugaba George W. Bush. A yayinda tsofon shugaban Amurka Bill Clinton ya gudanar da irin wadannan taruka har sau saba‘in, shugaba Bush, duka-duka tarukan nasa ba su wuce sau 15 ba. Ya kan yi bakin kokarinsa wajen halartar tarukan manema labarai idan ya hakikance cewar za a fuskance shi da wasu tambayoyin da ba zai iya amsa su ba. Shugaban na Amurka, daidai da mahaifinsa a misalin shekaru goma sha biyu da suka wuce, baya sha’awar hulda da manema labarai. A wani lokaci can baya sai da Bush ya ci mutuncin wani dan jarida a wani otel din cin abinci a Dallas, saboda ya bayyana mamakin yadda aka yi har mahaifinsa ya lashe zaben kasar ta Amurka. Galibi dai a duk lokacin da shugaban zai yi taro da manema labarai zaka tarar da mashawarciyarsa akan manufofin tsaro Condoleeza Rice da mukarrabinsa Carl Rove zaune a sahun gaba suna masu cancamza yanayin fuskokinsu a duk lokacin da shugaban ya fara daridari wajen amsa wata tambayar da aka gabatar masa a ba zata. A sakamakon haka sai an ba shi cikakken horo a fadar mulki ta White House kafin ya halaci duk wani taron da aka shirya masa tare da manema labarai. Alkaluma sun nuna cewar akalla kashi 90% na tambayoyin da za a fuskance shi da su ake koya masa yadda zai amsa su kafin a fara irin wannan taro. Da kuwa so samu ne da George W. Bush zai fi kaunar ganin an yi watsi da ragowar kashi 10% na tambayoyin saboda wahalar da ya kan sha fama da ita wajen amsa su. Misali daga baya-bayan nan John King, mai aikewa da tashar telebijin ta CNN rahotanni daga fadar mulkin ta White House ya fuskanci shugaba Bush da tambaya a game da zargin karerayin da aka ce an shiya a game da makaman kare dangi a kasar Iraki. Nan take shugaban ya shiga i’ina, kuma duka-duka abin da ya ce shi ne Saddam babban hadari ne. Da wuya ne shugaban ke iya amsa tambaya kai tsaye. Kuma yawa-yawanci ba ya iya rike sunayen shuagabanni ballantana ma na sauran mutane. Misali lokacin da aka tambaye shi a game da kame Ramzi Binalshib, Bush cewa yayi:

"Ramzi Al Binshib ko mene ne ma sunan nasa.Ka ga farce ni Ramzi idan na kira sunanka ba daidai ba."

To sai dai kuma ire-iren wannan katobarar ba ta ci wa akasarin talakawan Amurka tuwo a kwarya saboda dukkansu jirgi daya ne ke dauke da su. Shi kansa shugaba Bush ya fada a fili cewar ba ya karanta jarida, ya dogara ne kawai akan mashawartansa waje neman labarai, wai saboda kafofin yada labarai na da son kai. Wannan bayanin nasa kuwa yana mai yin nuni ne da irin kallon da ake wa ‚yan jarida a fadar mulki ta White House. Shugaba Bush ya kan yi amfani ne da wasu lafuzza na jawabansa domin amsa tambayoyin ‚yan jarida, kamar yadda wani dan jaridar yayi zargi a makon da ya gabata, inda ya fito fili yana mai fada wa shugaban cewar dukkan jawabanka iri daya ne babu wani banbanci tsakaninsu.