1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takon tsaƙa tsakanin Iran da ƙasashen Turai

March 22, 2010

Iran ta birkita tauraran ɗan Adam na ƙasashen Turai

https://p.dw.com/p/MZKQ
Taron Ƙungiyar Tarayar Turai a BrusselsHoto: DW/C.Stefanescu

Ministocin harkokin wajen Ƙungiyar Tarayar Turai sun fid da wani jawabi inda suka yi Allah wadai da matakin ƙasar Iran na birkita tauraran ɗan Adam da ke yaɗa labarai daga ƙasashen Turai. Jawabin na haɗin-gwiwa da suka fitar a yau Litinin a birnin Brussels ya yi kira wannan mataki na birkata tauaran ɗan Adam da ke yaɗa shirye-shiryen BBC da na Deutsche Welle tamkar mataki da sam da ba za a amince da shi ba. A don haka sun yi kira ga ƙasar ta Iran da ta daina yin hakan. Tun sanda aka shiga taƙaddama akan zaɓen watan yuni da Shugaba Ahmedinejad ya lashe ne dai mahukuntan ƙasar ta Iran suka ɗau matakan ƙara yin matsin lamba akan kafafen yaɗa labaru tare da cafke 'yan jarida da dama. A ranar 11 ga watan Fabarairu da ke zaman ranar bukin cika shekaru 31 na juyin-juya-halin Iran sai da aka birkita tauraran ɗan Adam da ke watsa shirye-shiryen tashoshin rediyo da na telebijan kusan guda 70 na ƙasashen waje.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Yahouza Sadissou Madobi