1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin nukiliya Ƙoriya ta Arewa

March 9, 2010

Ƙasar Koriya ta arewa ta yi gargaɗin ƙarfafa makamanta na Nukiliya

https://p.dw.com/p/MNgD
Makamai masu lunzami na Ƙasa Koriya ta ArewaHoto: AP

Ƙasar Koriya ta Arewa ta yi gargaɗin cewa zata ƙara ƙarfafa makamanta na nukiliya saboda abinda ta kira watsi da shugaba Barack Obama ya ke yi ga kiraye kiraye da ta ke yi na a samar da zaman lafiya.Hukumomin na Korea ta arewa sun ce yanzu haka sojojinsu na cikin shirin ko ta kwana yayin dakuma a share ɗaya sojojin Amirka da na Korea ta Kudu suka soma wani attisaye na haɗin guywa da ya tatara dakarun ƙasashen biyu sama da dubu arba'in.Wannan attisaye da dakarun ƙasashen biyu suke yi a kowace shekara na zaman abin ɓacin rai dakuma tsokana ga ƙasar Korea ta arewa.

Wata kakakin ministan harakokin waje ta Korea ta ce matuƙar Amirka zata cigaba da yi masu barazana ta soja da ta tatalin arziki to kam zasu cigaba da dagewa akan ƙera makaman nukiliya. ƙasar ta Korea dai ta fice daga cikin kwamitin shawarwarin sulhu na ƙasahe shidda waɗanda suka haɗa da cina da Amirka da Rasha da Japon da Korea ta ƙudu shekara guda da ta gabata domin nuna damuwarta akan takunkumin karya tatalin arziki da majalisar ɗinkin duniya ta ƙaƙabamata a shekara ta 2009 akan gojin da ta yi na makamin nukiliya

Mawallafi: Abdurahamane Hassane

Edita : Abdullahi Tanko Bala