1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takunkumi ba shi ne masalaha ba

October 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bueq

Shugaban hukumar Majalisar ɗinkin duniya mai lura da hana yaɗuwar makaman nukiliya Mohammed el- Baradei ya yi kira da a sami tattaunawa ta fahimtar juna da ƙasashen Koriya da arewa da Iran a game da shirin su na nukiliya. Yayin da yake jawabi a Washington, el-Baradei ya yi kashedin cewa ɗaukar matakin takunkumi zai kara sanya ƙasashen biyu ɗaukar tsatsauran mataki a kan manufofin su. Yace har yanzu bai gamsu da cewa Iran na yunƙurin sarrafa makaman nukiliya ba, yayin da a waje guda kuma yace ya yi Imani zaá iya cimma daidaito da Koriya ta arewa a game da shirin ta na nukiliya. A cikin wannan watan ne dai kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya ya kaɗa ƙuriár sanyawa Koriya ta arewa takunkumin karya tattalin arziki a sakamakon gwajin da ta yi na makaman nukiliya. Mai yiwuwa ne ita ma Iran ta fuskanci sanya mata takunkumi saboda bujirewa uamarnin kwamitin tsaron na kin dakatar da bunƙasa makamashin Uranium.