1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takunkumin MDD ga ƙasar Iran

June 8, 2010

Majalisar Ɗinkin Duniya ta share fagen ƙaƙaba ma Iran sabon takunkumin karya tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/NlZp
Zauren mashawarta ta MDDHoto: AP

Komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya cimma matsaya game da jami'an gwamantin Iran da kuma cibiyoyin sarrafa makamashinta da za a iya ƙaƙaba ma takunkumi. Jakadun ƙasashe biyar da ke da kujeran dindindin a komitin da kuma Jamus a taron share fage da suka gudanar a yau, sun tsayar da shawara game da salon takunkumin karya arziki da za su sanya ma Iran a zamansu na gobe laraba.

Takunkumin da zai zama irinsa na huɗu ga ƙasar ta Iran, zai shafi dukkanin manyan jamai' an gwamanti da ke da hannu wajen sarrafa makamashin na Urinium da kuma bankunan da ke samar da kuɗin gudanar da wannan aiki. A lokacin da ya ke mayar da martani, shugaba Mahmud Ahmadinejad ya ce ƙasarsa za takatse duk wata hulɗa da ƙasashen yammacin duniya  idan aka ƙaƙaba mata wani sabon takunkumi.

Waɗannan ƙasashen dai na zargin Iran da yunƙurin bunƙasa makamashin Uranium da nufin ƙera makaman ƙare dangi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza Sadissou