1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Talakawan Legas sun samu galaba kan gwamnatin jihar

June 21, 2017

Babbar kotun jihar Legas ta dakatar da gwamnatin jihar daga ci gaba da rusa gidajen talakawa ba bisa ka'ida ba tare da umarnin komawa teburin sulhu don kare hakkin talaka.

https://p.dw.com/p/2f8Is
Nigeria schwimmender Slum in Lagos
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/M. Elshamy

A zamanta na wannan Laraba, kotun da ke Igboshere ta tabbatar da cewa, gwamnatin Legas da ke Kudu maso Yammancin Najeriya ta yi karan tsaye ga dokar kasa, musamman ta cin zarafin talakawa wadanda ta rusawa gidajensu ba tare da basu wa'adi ba.

Misali idan aka duba wadanda ke wuraren da ke kusanci da bakin teku da gwamnati ta lalata tare da haifar da rashin wuraren kwana da ya shafi dubban jama'a. Wurare kamarsu Otodo Gbame da Ikorodu da Otumara da Okun Agban sun fada cikin wannan taskun.

Comrade Mohammed Zanna da ke zama daya daga cikin mazauna wadannan yankuna ya ce akalla mutane dubu 30 ke zaune a wurin kuma "idan aka kore su ko aka tada su daga wurin, to ai wani matsugunin za a je a kirkiro a wani wuri." Saboda haka Mohammed Zanna ya goyi bayan da a zauna kan teburin sulhu da mahukuntan jihar ta Legas. 

Wannan matsala dai ta shafi matsuguni sama da 39 duk kuwa talakawa ne da ke zaune a wadannan yankunan.

Barrister Omotayo Enujiga ita ce mai kare hakkin mazauna wannan yanki a gaban kotu da ta bayyana hukuncin kotun da cewa ya yi armashi na komawa teburin sulhu da gwamnati don samun mafita. Su ma mazauna wadannan matsugunan talakawan sun yi farin ciki da hukuncin kotun, sun kuma yi fatan gwamnati za ta mutunta hukuncin kotun. 

Gwamnatin jahar Legas ta ce tana daukar matakin rusau ne saboda dalilai na tsaro da kuma kare muhalli.