1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban sun karbe wani yanki a Afghanistan

Zulaiha Abubakar
March 1, 2017

An wayi gari da tashin bama-bamai a garin Baglan, abin da yayi sanadiyyar rasa rayuka da dama wanda suka hada da mata da kananan yara.

https://p.dw.com/p/2YUac
Afghanistan Sicherheitskräfte nach einem Anschlag in Kabul
Hoto: Reuters/O. Sobhani

'Yan Kungiyar ta'adda ta Taliban sun karbe wani yanki a Afghanistan kamar yadda wani mazaunin arewa maso gabashin garin Baglan kusa da in da yan ta'addan suka yi sansani ya shaida wa manema labarai.An wayi gari da tashin bama-bamai abin da yayi sanadiyyar rasa rayuka da dama wanda suka hada da mata da kananan yara bayan yan ta'addan sun tsare duk wata kofa da mutane za su iya tserewa kamar yadda kakakin kungiyar 'ta'addan ta Taliban ya rubuta a shafin Twitter cewar a halin yanzu suna tsare da jami'an tsaro goma sha uku sannan sun harbe mutum uku. Yankin Baglan ya dade yana  fama da irin wannan farmaki na 'yan Taliban a afghanistan.