1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ta yi tayin sulhu

February 14, 2018

Kungiyar Taliban ta ce ba zata ki zaman sulhu don kawo karshen yakin kasar Afghanistan ba, sai dai ta yi gargadin cewa kalaman nata ba sa nufin alamu ne na gajiyawa ba.

https://p.dw.com/p/2sgl4
Afghanistan Wakhan Nomaden Familie
Hoto: Getty Images/G.Abbas

Kungiyar 'yan tawayen Taliban ta kasar Afghanista, ta ce ba zata ki zaman sulhu don kawo karshen yaki ba a kasar, sai dai ta a share guda yi gargadin cewa kalaman nata ba sa nufin alamu ne na gajiyawa ba. Matakan tsananta luguden wuta ta sama da Amirka ke yi kan mayakan Taliban din tun cikin watan Agustan shekarar da ta gabata dai, ya tilasta mayakan bari wasu gundumomi da ma wasu manyan lardunan da suke rike da su a Afghanistan din.

Sai dai mayakan na tawaye na ci gaba da iko da wasu wuraren, inda suke ma maida martani ga zafafan hare-haren da AMirka ke kaddamarwa a kansu, inda ko cikin makonnin da suka gabata sun kaddamar da wasu munanan hare-haren a Kabul da mutane akalla 150 suka halaka.