1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafin raya kasa ga wasu kasashe 10 a Afrika

Ibrahim SaniDecember 27, 2005

Kungiyyar Eu ta bada sanarwar tallafawa wasu kasashe goma na Afrika da masu gidan rana

https://p.dw.com/p/Bu31
Hoto: AP

Wannan sanarwa ta kungiyyar ta Eu data fito a jiya litinin,kungiyyar ta Eu tace tayi hakan ne don tunawa da miliyoyin mutanen dake cikin hali na ka ka ni kayi a matalautan kasashe na nahiyar ta Afrika.

A cewar kwamishinan bada tallafi na raya kasa na kungiyyar ta Eu, Louis Michel,a yayin da kungiyyar ta Eu take tunawa da mutanen da bala´in igiyar ruwa ta tsunami tayi wa lahani a matsayin shekara guda cif da faruwa, akwai bukatar kungiyyar ta kuma tuna da hali na kunci da wasu miliyoyin mutane ke ciki a wasu matalautan kasashe na nahiyar ta Afrika.

Ire iren wadan nan kasashe da zasu samu wannan tallafi a cewar Louis Michel, da yawa daga cikin mutanen kasashen sun fuskanci bala´oi iri daban daban dake da nasaba da fari da ambaliyar ruwa da kuma cututtuka na kwari da dangogin su.

Wadannan kudade da yawan su ya tasamma Yuro miliyan 165 da digo 7, kwatankwacin Dalar amurka miliyan 196 da digo 9 za a rarraba sune a tsakanin wadannan kasashe goma a sabuwar shekara mai kamawa ta 2006.

Kasashen da zasu ci gajiyar wannan tallafi dai sun hadar da kasar Sudan da Kongo da Burundi da Chad da Tanzania da Uganda da Liberia da Ivory Coast da Madagascar da kuma Comoros.

Daga dai cikin wannan jumla ta sama da muka ambata, kasar Sudan zata samu mafi tsoka daya tasamma yuro miliyan 48, wanda a cewar hukumar ta Eu za´ayi amfani dasu wajen inganta rayuwar mutanen yankin Darfur da suka sha fama da yaki da kuma rikice rikice a hannu daya kuma da tsugunar da wadanda suka rasa gidajen kwanan su a sakamakon wadannan bala´oi.

Kasar Kongo wacce har yanzu take fama da tashe tashen hankula na yan bindiga dadi, duk kuwa da kokarin da ake na wanzuwar zaman lafiya a kasar, an kiyasta cewa zata sami tallafi na yuro miliyan 38, don inganta harkoki na lafiya,tare da inganta matsugunan yan gudin hijira.

Ita kuwa kasar Burundi zata sami yuro miliyan 17, a yayin da kasar Liberia da kwana kwanasn nan ta kama turbar mulkin dimokradiyya zata sami yuro miliyan 16 da digo 4.

Rahotanni dai daga kungiyyar ta Eu sun tabbtar da cewa kasar Uganda zata samu yuro miliyan 15 ne sai kasar Chad mai yuro miliyan 13 da digo 5, kana kasar Tanzania kuma ta samu tallafi na yuro miliyan 11 da digo biyar.

Bugu da kari rahotannin sun kuma nunar da cewa kungiyyar ta Eu da a yanzu ke matsayin kungiyyar dake a mataki na farko a yawan bada tallafi na raya kasa, tuni ta amince ta kara yawan kudaden da take kashewa a matsayin tallafin raya kasa a sabuwar shekara ta 2006 mai kamawa.

Daga cikin wannan kari da kungiyyar ta Eu take son yi a sabuwar shekarar, ta kuma amince da mika rabin karin da tayi izuwa kasashe na nahiyar Afrika.