1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

220910 Solidarpakt Aufbau Ost kurz

September 28, 2010

Gwamnatin Jamus za ta cigaba da bada tallafin zumunta domin raya gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/PPG4
Tutar kasa ta hadin kan JamusHoto: picture-alliance/ZB

A lokacin sake hadewar gabashi da yammacin Jamus a shekarar 1990, shugaban gwamnati Jamus na wancan lokaci Helmut Kohl ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta cigaba da nuna zumunta ga yankin gabashin kasar domin taimaka mata ta bunkasa. Ya zuwa yanzu dai aikin sake gina gabashin kasar ya ci tsabar kudi fiye da euro miliyan dubu ɗaya. Gagarumin aikin da har yanzu ba'a kai ga kammala shi ba. A shekarar 2019 ne dai za'a kawo karshen tallafin raya kasa da al'umar yammacin ke bayarwa ga gabashin kasar.

Ga duk mutumin da ya bi hanyoyin biranen Dresden ko Quedlinburg ko Postdam ko kuma Stralsburg zai ga irin bunkasa da kuma sauyin da aka samu a wadannan wurare. Wannan nasara ta samu ne sakamakon alkawarin da tsohon shugaban gwamnatin Jamus Helmut Kohl ya yiwa gabashin kasar a shekarar 1990 cewa za'a cigaba da taimakawa gina yankin har na tsawon shekaru Ashirin. Zancen da ake yanzu haka aikin sake gina gabashin kasar ta Jamus ci tsabar kudi euro Miliyan dubu daya da dari uku. Theo Waigel tsohon Ministan kudi na tarayya daga shekarar 1989 zuwa 1998 yace wannan shine gagarumin taimakon zumunci mafi girma da aka taba yi a Jamus baki daya. Yace yan siyasa a kasar bama kawai sun ci moriyar wannan zumunta bane kadai sun ma koyi darasi daga gare ta.

Cross Border Leasing Dresdner Straßenbahnen verleast
Birnin Dresden ya bunkasa bayan hadewar gabashi da kudancin JamusHoto: picture-alliance / ZB

" Wasu yan shekaru da suka wuce shugaban wani kamfani na Amirka ya yi min tambaya yace dani Theo ai kuwa ina gani kudirin da kuka dauka na tallafawa yankin gabashin kasar akwai kasada a cikinsa ko ? Da ya fadi wannan kalma sai na ji ya sosa min rai, to amma sai na ce da shi haka ne, an dauki tsawon lokaci kuma ya ci kudi fiye da yadda muka yi tsammani, wannan gaskiya ne to amma mutane miliyan goma sha takwas dake zaune a wannan yanki suna zaune bisa tafarki na dimokradiya cikin jin dadi da walwala wannan shine burin mu".

Ba wai sake gina jihohin da zuba makudan kudade a aikin sake gina abubuwan bukatun rayuwar jama'a ke da rikitarwa da kuma jan kudi masu yawa ba a'a, baki daya rugujewar tattalin arzikin yankin shine ya haifar da tabarbarewa da rashin aiki da suka yi katutu a gabashin Jamus, saboda haka ya zama wajibi a taimakawa yankin. Sai dai kuma duk da makudan kudaden da aka kashe a gabashin kasar ta Jamus har yanzu cigaban tattalin arzikin yankin bai kai na yammacin kasar ba.

Hasali ma idan za'a raba abin da gabashin kasar ke samu a shekara da yawan al'umar yankin, bai wuce kashi 71 cikin dari na abin da dan yankin yammaci zai samu ba. Ta fuskar tallafi na jin dadin rayuwa da walwala kuwa, abin da gwamnati ke sawa a wannan bangare a kasafin kudi ga yankin gabashi ya fi na yammacin kasar da kimanin kashi Ashirin cikin dari idan aka kwatanta su. Sai dai a cewar Firaminista na karshe a gabashin Jamus Lothar Maiziere ya musanta cewa hadewar yankunan biyu shine ya haifar da wannan koma baya.

Helmut Kohl in einer Menschemenge
Tsohon shugaban gwamnatin Jamus Helmut Kohl a lokacin bikin hadin kan kasaHoto: picture-alliance / dpa

" Babu shakka muna da matsaloli masu yawa da suka danganci hadin kan kasa. To amma hakikanin gaskiya wadannan matsaloli suna da nasaba ne da ayyukan dake gudana na dunkulewar duniya baki daya. Alal misali an sami sauye sauye da dama na fasalin tattalin arzikin duniya, saboda haka akwai matsaloli da suka danganci hadewar amma ba hadewar ce ke da matsala ba".

Babbar matsalar dai ita ce dogaron da yankin gabashin ke yi akan yammaci musamman ta fuskar kudade. A waje guda dai tallafin zumunta na raya kasa zai cigaba kamar yadda gwamnatin tarayya ta tsara har ya zuwa shekarar 2019, wato ma'ana nan da yan shekaru masu zuwa za'a danka wasu makudan kudade ga gabashin kasar, bayan nan kuma zata cigaba da kula da kanta kamar dai yadda a yanzu yake wakana a yammacin kasar ta Jamus.

Mawallafa : Sabine, Kinkartz/Abdullahi Tanko Bala

Edita : Yahouza Sadissou Madobi