1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tantanawa a game da girka sabuwar gwamnati a ƙasar Isra´ila

April 2, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3L

Shugaban kasar Isra´ila Moshe Katsav, ya fara tantanawa da jami´yun siyasa, domin girka sabuwar gwamnati, bayan zaɓen yan majalisun dokoki da a ka gudanar.

A sahiyar yau, ya gana da praministan riƙwan ƙwarya Ehud Olmert, wanda jami´yar sa ta Kadima, ta zo sahun gaba da kujeru 29.

Daga bisani, shugaban ƙasar zai gana, da jam´iyar yan Labor da ta zo sahu na 2.

Kamar yada dokar ƙasar Isra´ila ta tanada, shugaba ƙasa ke da yaunin naɗa Praminista, da zai hito daga jam´iyar da ta fi yawan yan majalisa.

Kusan babu shakka, Ehud Olmert, zai riƙe wannan matsayi.

Saidai ,akwai alamun a fuskanci saɓanin ra´ayoyi, tsakanin Kadima, da Jam´iyar Labor, mussamman a wajen rabon muƙamai masu mahimanci, da su ka haɗa da ministan harakokin waje, da kuma na passalin kuɗi.

Amma, a jawabin farko, da yayi bayan gajera nasara da jamiyar kadima ta samu, Ehud Olmert, ya ce a shirye ya ke ,ya biya bukatocin abokan kawance, na Labor.

Tantanawa da zata ɗauki tsawan kwanaki, na gudana a yayin da har yanzu Praminista Ariel Sharon da ya girka jam´iyar Kadima ke kwance assibiti, rai kwakawai, mutu kwakwai.