1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tantanawa tsakanin Angeller Merkel da Tabon Mbeki

Yahouza S. MadobiJuly 8, 2006

Shugabar gwmnatan Jamus Angeller Merkel ta karɓi baƙunci Tabon Mbeki na Afrika ta kudu

https://p.dw.com/p/BtzL
Hoto: AP

Shugaban Afrika Afrika ta kudu Tabon Mbeki, a matyasin sa na shugaban ƙasar da zata karɓi ludayi, na shirya gasar cin kofin ƙwallon kafa ta dunia, a shekara ta 2010, ya gana jiya asabar, da shugabar gwmnatin Jamus Angeller Merkel, a yayin da ya rage kwana ɗaya rak,a yi gasar ƙarshe da zata haɗa ƙungiyar ƙwalon ƙafa, les Bleus ta France, da la Squadra Azzurra ta ƙasar Italia, nan gaba a yau.

Bayan ganawar, magabatan 2, sun yi taron manema labarai.

Tabon Mbeki, yayi anfani da wannan dama, inda ya tabatar da cewa, Afrika ta Kudu a shire ta ke, ta karɓi gasar cin kofin ƙwallan ƙafa ta dunia, a shekara ta 2010.

Ya ce,Gwamnati tayi tanadin kuɗade, waddattatu, domin cimma nasara tsari mai inganci, duk da cerar, wannan shine karo na farko, da nahiyar Afrika zata karɓi gasar.

Kyaukayawan tsarin ,da Jamus ta yi, zai zama darasi ga Afrika ta kudu domin a tsawan watani masu yawa wakilan sun zauna a nan Jamus, domin bi sau da ƙafa yada a ke gudanar da shirye shiryen.

Mbeki ya ƙara da cewa:

Ina mai farin cikin cewa Franzbecken Bauer, shugaban komitin tsare staren gasar Jamus, da sauran abokan aikin sa sun cimma burin da su ka sa gaba.

Sannan kuma,sun yi alkawarin bada gudummuwar ga kasar mu, da ke da yaunin tsatrin gasa ta gaba.

Mun samu darasi ƙwaƙwara daga Jamus, godiya ta tabatta ga Shugabar gwamnati.

Duk da ƙorafe ƙorafe da zargin da kafafin sadarwa ke yi a kan cewar Afrika ta kudu, ba za ta iya cimma nasara shirya gasar ba, hukumar FIFA, ta ce ba ta da shakun komai a game da haka.

A nata gefen shugabar gwmanatin Ƙamus Angeller Merkel, ta ƙara ƙarfin gwiwa ga Tabon Mbeki kamar haka.

Yan magana kan ce: a na shirya wasa na gaba, da za ran an kammalla wasan da ya gabata.

Kuma taikamon da Jamus zata ci gaba da baiwa Afrika, ya dogara ga nasara da za a samu, a Jamhuriya Demokradaiyar Kongo.

Saboda haka, daga ɓangaren Jamus, mu na jiran sakamako na gari, ta la´kari da cikkaken haɗin kai, da mu ka samu ta ɓangarori da dama.

Angeler Merkell da Tabon Mbeki, sun yi anfani da wannan dama, inda su ka tantana kann batutuwan da su ka shafi halin da a ciki a yankin Darfur na ƙasar Sudan, da kuma taron G8 da za a gudanar a kasar Rasha, a mako mai zuwa.