1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Afirka za ta kara wakilai a Burundi

Salissou BoukariFebruary 27, 2016

Shugaban tawagar kungiyar Tarayyar Afirka da ta kai ziyara a Burundi Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya sanar da batun kara masu sa ido don kare hakin dan Adam a Burundi

https://p.dw.com/p/1I3Ow
Ausschnitt Jacob Zuma in Burundi
Jacob Zuma a BurundiHoto: Reuters/E. Ngendakumana


Cikin wata sanarwa da ya fitar, jagoran tawagar kuma Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya ce Tarayyar Afirka za ta zuba masu sa ido kan kare hakin dan Adam 100 da kuma sojoji kwararru kan harkokin tsaro su ma guda 100 domin bi sau da kafa yadda lamura ke gudana a kasar ta Burundi.

Tawagar ta Tarayyar Afirka ta hada da shugaban kasar Mauritaniya da na Senegal, da Gabon, sannan da Firaministan Habasha inda suka kasance a kasar ta Burundi a ranakun Alhamis da Jummaa domin saduwa da bangarorin kasar da ke cikin tsaka mai wuya tun watanni 10da suka gabata.