1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da bai wa Girka rance

Suleiman BabayoJuly 17, 2015

Daukacin kasashen Tarayyar Turai suka amince da kudirin ceto tattalin arzikin kasar Girka

https://p.dw.com/p/1G0o8
Deutschland Bundestag Sondersitzung Griechenland
Hoto: Reuters/A. Schmidt

A wannan Jumma'a Kungiyar Kasashen Tarayyar Turai ta amince da shirin kajeran lokaci na ceto tattalin arzikin kasar Girka, daga mako mai zuwa, yayin da kasashe masu amfani da kudin bai daya na Euro za su ci gaba da tsara hanyoyin magance matsalar ta Girka.

Daukacin mambobin kungiyar 28 suka amince da bai wa kasar ta Girka Euro milyan dubu-7, bayan shawo kan kasashen Birtaniya da wadanda ba sa cikin kudin na Euro cewa babu wata kasada da za su fuskanta.

Tun farko Majalisar dokokin kasar Jamus ta Bundestag da gagarumin rinjaye ta amince da shirin ceton tattalin arzikin kasar Girka, domin tabbatar da matakan da kasashen Turai na kare Girka. A wannan Jumma'a majalisar ta jefa kuri'ar amincewar, inda 'yan majalisa 439 suka amince sannan 119 suka nuna rashin amince, kana 'yan majalisa 40 suka rowar kuri'unsu. Tun farko Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci samun goyo baya kan matakin.