1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarayyar Turai ta soki zaben Rasha

Salissou Boukari
March 19, 2018

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da damuwarta kan abin da ta kira take hakkoki da masu sa ido da ta tura na OSCE a zaben kasar Rasha suka gano, inda suka ce zaben ya gudana ba tare da wani babban abokin hamayya ba.

https://p.dw.com/p/2ubBP
EU-Außenministertreffen in Brüssel
Hoto: picture-alliance/dpa/V.Mayo

Yayin wata hira da aka yi da shi, Shugaban tawagar ta Tarayyar Turai a zaben na Rasha Jan Petersen ya yi tsokaci inda yake cewa: " An fuskanci saba dokoki sosai, mun ga kuri'un zabe ba bisa ka'ida ba a birane bakwai na kasar ta Rasha. Sai dai a fannin tsarin zabe muna iya cewa lamarin ya gudana yadda ta kamata."

Sai dai kuma sanarwar ta Tarayyar Turai ta ce ta gano cewa babu 'yancin walwala a kasar ta Rasha, musamman ma wajen shirya taruka, ko ma kafa kungiyoyi masu zaman kansu, da 'yancin fadar albarkacin baki, aibn da ya hana samun mutane da dama masu niyar tsayawa takara.

Da karshe Tarayyar Turai ta yi Allah wadai ta zaben da aka yi a yankin Kirimiya wadda take kan bakanta kan adawa da kwatar yankin da Rasha ta yi.