1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mataki kan bakin haure a Turai

February 3, 2017

Kasashen na kungiyar Tarayyar Turai na taro a Malta inda suka dauki wasu kudirori domin dakile bakin haure masu kwarara zuwa nahiyar domin samun rayuwa mai inganci.

https://p.dw.com/p/2WvI6
EU-Gipfel auf Malta | Gruppenbild
Hoto: Reuters/Y. Herman

Shugabannin kungiyar kasashen Tarayar Turai da ke taro a kasar Malta sun amince da wasu kudirori 10 da za su taimaka dakile kwararrar bakin haure daga tekun Bar Rum, kamar yadda wasu majiyoyin diplomasi suka tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Jamus, DPA. A ciki akwai taimakon mahukuntan Libiya domin tabbatar da tsaro. Dubban mutane kan dauki kasadar ketere teku domin samun wata madafa ta rayuwa a kasashen Turai.

Sannan shugabbanin suna duba kalubale bayan ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar ta Tarayyar Turai, gami da yadda sabuwar gwamnatin Amirka karkashin shugaba Donald Trump ke zama barazana ga kungiyar. Tuni shugaba Francois Hollande na Faransa ya matsin lamba da kungiyar Tarayyar Turai ke fsukanta daga Amirka ba abu ne da za a amince ba.