1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin CN Tower ta Toronto

Abba BashirFebruary 14, 2006

Takaitaccen Tarihin Tashar watsa shirye-shirye ta CN Tower

https://p.dw.com/p/BvVY
The CN Tower
The CN TowerHoto: dpa

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon, ta fitone daga hannun Malam Nura Yahaya , Mazauni a Jidda daga can kasar Saudiyya.Malamin ya ce dao Allah ina so ku bani Tarihin Dogon gininan na Birnin New york a kasar Amurka, wanda aka fi sani da suna ( The Empire State Building ) a Turance?

Amsa. To tabbatacciyar magana ce cewar , Talabijin na daya daga cikin abubuwan mamaki da a cikin dan lokaci kankane ta caja rayuwar alumma a Karni na 20 .Kuma aduk inda Gidan Talabijin yake, zaa samu akwai wata doguwar Eriya wadda ta ke inganta yada shirye-shirye ta akwatunan talabijin.

To awajen shekarar 1960 gidan talabijin na birnin Toronto da aka fi sani da suna (Soaring Skyline) ya fara fuskantar matsaloli dan gane da yada shiye-shirye ta akwatunan Talabijin.Saboda maganadisun da yake da alhakin yada shiye-shiryen ya bada tangarda wadanda suka hada da mai da hotuna su zama wasu dodanni –dodanni, a akwatunan Talabijin. Sakamakon sai hukumar kula da harkokin jiragen kasa ta kasar Canada wato (Canadian National Railway) ko kuma CN a takaice,ta bayar da shawarar cewa a gina wata hasumiya mai tsawon gaske don yada shirye-shirye wadda zata kere tsawon duk wani gini da yake a birnin Toronto, wannan shine dalilin da ya haifar da samuwar CN Tower, a takaice.

kamfanin ciniki na birnin Toronto ne ya shirya yadda asalin wannan katafariyar hasumiya zata kasance, inda a ciki ya lissafa irin kwararrun Injiniyoyin da za su bada gudunmowarsu wajen zana da kuma gina wannan Hasumiya. Sakamakon haduwar wadannan kwararrun Injiniyoyi ne kuma aka fitar da zanen siffar wannan doguwar hasumiya wadda take da tsawon kafa 1,815.5 An dai gina wannan tasha ta yada shirye-shirye ne a siffar hasumiya irin ta masallaci dai wadda aka sani, to amma ita wannan dayake an yi ta ne domin yada shirye-shirye sai aka yi ta mai tsawon gaske kuma da hawa-hawa-har guda uku.

Hawa na farko shine mai siffar hasumiya cikakkiyainda yake da tsawon kafa 1100,daganan sai aka yi mata dauri ta hanyar gina wani abu kamar tuntu, kuma aka nade tuntun da gini kamar rawani, sannan aka dora sahu na biyu na ginin shima da aka kai inda ake so wato kafa 365 sai aka dada gina wani tuntun, amma shi baa yimasa rawaniba, sannan aka dora gini na karshe,wanda yake da tsawon kafa 335, kuma ginin yana tafiya a tsukene, kamar dai zaa iya siffanta shi da siffar babban baki na (Y) ta rubutun boko.

An dai kafa harsashin ginin wannan tashar yada shirye-shirye ne a shekarar 1973, kuma kamfanin da ya yi wannan gini sai da ya hako kasar da nauyinta ya kai kimanin Ton 62000 a yayin haka ramin da zaa kafa harsashin ginin. Inda aka haka ramin da zurfinsa ya kai tsawon kafa 50. sannan aka zo aka shiya rodina aka kuma zuba kankare da kaurin sa yakai kafa 22 .wato nauyin gaba dayan hasumiyar kenan idan aka kammalata.

Shi kansa harsashin ginin wannan hasumiya sai da aka dauki watanni hudu cur ba dare ba rana kafin a kammala shi, kuma ita kanta wanna hasumiya tamkar wani kalubale ce ga Injiniyoyi na gine-gine, domin kuwa kafin a gina ta ,ba a taba samun wani gini mai tsayi wanda aka yi shi da kankare kamar ita ba . Domin kuwa hawa na uku na hasumiyar , wani jirgin sama na Helikofta ne ya dora shi, inda ya dauki kann hasumiyar da aka gina a kasa mai nauyin Ton 47 ya dora bisa ginin, kuma ya rinka daukar sauran kayan daya bayan daya yana sakawa a kololuwar hasumiyar har aka kammala ginin. Kuma an rufe kololuwar hasumiyarne da gilashi domon a kare kayayyakin da aka sa daga zubar kankara a lokacin sanyi. To amma dai an kammala ginin wannan hasumiyar ne a shekarar 1975 kaga kenan shekaru biyu cur aka dauka ana gina wannan katafariyar hasumiya.

Wannan Hasumiya dai ta ci kudi da suka kai $ Miliyan 57.wajen ginata.kuma wannan ya hada harda wata kariya da Injiniyoyi suka gina wadda zata rinka kare wannan hasumiya daga barazanar iska ko kuma guguwar da gudunta bai wuce mil 260 ba, a awa daya ba.

A Yan shekarun da suka wuce , Hasumiyar na da Injina guda biyu musu jigilar Mutane daga sama Zuwa kasa, to amma sakamakon karuwar masu ziyara yasa dole aka kera wani bene mai hawa 2579 aka je aka kafa shi a cikin ginin hasumiyar.

To ammadai a gabakidaya babban abin farincikin shine , yadda kwalliya ta biya kudin sabulu, sakamakon gina wannan hasumiya, domin kuwatun daga lokacin da aka kammala gininta, Gidan Talabijin na Skyline ya rabu da fuskantar tangarda , kuma ya zama gidan talabijin mafi daukaka da inganci, ya kuma zama abin kwaikwayo a Duniya.