1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Fernando Pereira

Abba BashirSeptember 26, 2005

Takaitaccen Tarihin Fernando Pereira

https://p.dw.com/p/BwXN
Tutar Kasar Sao Tome and Principe
Tutar Kasar Sao Tome and Principe

Masu sauraron mu assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardun ku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya-Fatawar mu ta wannan makon ta fito ne daga hannun mai sauraron mu a yau da kullum Muhammed Ibrahim, dalibi a jami’ar Bayero ta Kano a tarayar Nigeria,mai sauraron namu cewa yayi yana so filin amsoshin takadun ku ya bashi takaitacen tarihin mutumin da ya jagorancin juyin mulkin da aka yi a tsibirin Sao Tome wato Fernando Pereira sanan kuma wane hali yake ciki a halin yanzu.

Amsa-An haifi Fernando Pereira a garin Vermelha na kasar Portugal a cikin watan Octoba na 1962,ya sami iliminsa na jami’a a fanin injiniya a jami’ar Lisboa ta kasar Portugal a shekara ta 1985,a halin yanzu kuma ya sami zama Parfesa a fanin al’amuran da suka shafi kimiya da fusaha ya kuma zama mutumin da yake bada gudunmawa a fanin binciken ilimin kimiya da fasaha na jami’ar kasar Portugal.

A shekara ta 1990 Fernando ya sami lambar girmamawa ta IBM ta kasar Portugal a sabili da irin gudunmawar da ya bayar a fanin cigaban kimiya da fasaha.

Fernndo Pereira ya shiga aiyuka irin na soji tun bayan da ya kammala makaranta,tun daga wanan lokaci ne ya nuna sha’awarsa ta samun gurbin karatu a kasahen ketare amman kuma hakan ya gagara,daga wanan lokacin ne ya shiga aiki na sojan sa kai.

Mafarkin da Fernando ya dade yana yi ya baiyana a zarhiri ne a lokacin da ya shiga aikin soji sosai,inda har ma aka baiyana cewar ya sami horo a fanin aiyukan soji a kasahen Angola,Cuba,da kasar Portugal ya kuma zama mutumin da ya ziyarci kasahen Africa da dama.

A matsayinsa na soja mai lura da hulda da kasahen duniya da kuma baiwa soji horon sanin makamar aiki,ya taba samun lamba ta yabo daga hukumomin soji na kasar Gabon.

A safiyar ranar 16 ga watan Yuli na shekara ta 2003 aka wayi gari soji sun kifar da gwamnatin kasar Sao Tome and Principe.Wata rudunar soji dake karkashin jagorancin Major Fernando Pereira dake shugabantar makarantar horas da aiyukan soji ta tsibirin Sao Tome and Principe ne suka kifar da gwamnatin.A wanan rana ne aka rika jin karar amon harbin bindigogi a kan titunan kasar ta Sao Tome da kasar Portugal ta taba yiwa mulkin malaka.

A lokacin da aka gudanar da juyin mulkin na Soji a tsibirin Sao Tome,soji ne suka karbe ragamar tafiyar da baban banki na kasa da kuma gidajen Radio da Talabijin,filayen jiragen sama da muhimman wurare inda soji suka umarci yan majalisar ministocin kasa da yan majalisar dokoki da su baiyana a hedikwatar yan sanda ta Sao Tome.

A lokacin wanan juyin mulki ne soji suka kama Firaministan kasar ta Sao Tome wato Maria das Neves da kuma sauran yan majalisar ministoci dake lura da sassa na arzikin mai da Allah ya horewa kasar ta Sao Tome.

Ranar da aka wayi gari soji sun yi juyin mulki a tsibirin Sao Tome,basu iya fitowa fili sun baiyana dalilan da suka sanya suka kwace mulki ba.To amma kuma wasu na cewa soji sun yi wanan juyin mulki ne don nuna fushin su ga gwamnati game da dalilan da suka sanya ba’a biya su albashin su ba yadda ya kamata ganin cewar arzikin mai da Allah ya horewa kasar ya kara bunkasa.

Duk kuwa da arzikin man da Allah ya horewa kasar Sao Tome and Principe,to amman kuma alumarta sun cigaba da zama cikin hali na kangin talauci da kuncin rayuwa.

Rahotanin da suka fito a dangane da juyin mulkin sojin da aka yi a Sao Tome and Principe sun baiyana cewar sai da jakadan kasar Portugal a kasar wato Mario de Jesus Santos ya bukaci ganawa da shugabanin da suka shirya wanan juyin mulki,don tabatar da ganin an shawo kan lamarin.

A ranar 17 ga watan Yulin shekara ta 2003,madugun yan tawaye,Major Pernando Pereira yayi magana da shugaba Obasanjo na Nigeria ta wayar tarho,inda ya amince da ya gana da wakilan Nigeria masu shiga tsakani.Tun daga wanan lokaci ne ya bada umarnin a bude filayen jiragen sama na kasar,koda yake a baya ‘yan tawayen da suka yi juyin mulkin na sun ce ba zasu tattauna da wakilan Nigeria ba.

An gudanar da juyin mulkin tsibirin na Sao Tome ne a lokacin da shugaban kasar Fradique de Menezes ke halartar wani baban taro na kasahen Africa a birnin Abuja.

Kasahe da dama na duniya sun yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a kasar Sao Tome,inda har ma a mayarda martani da kasahen duniya suka yi Shugaba Obasanjo ya bukaci sojin da suka yi juyin mulkin na Sao Tome,su gaggauta mika ragamar mulki ga zababbiyar gwamnatin kasar.

Daga karshe dai gwamnatocin kasahen Africa sun yarda da dalilan da masu juyin mulkin na tsibirin na Sao Tome suka bayar,sakamakon haka daga karshe an yiwa masu juyin mulkin afuwa.

Muna fata mai sauraron namu ya gamsu.