1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Ganuwar Kasar Sin

Abba BashirSeptember 4, 2006

Bayani akan Kasaitacciyar Ganuwar Kasar Sin

https://p.dw.com/p/BvVH
Kasaitacciyar Ganuwar Chaina
Kasaitacciyar Ganuwar ChainaHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun,malam Ali Na-jume, Argungu, Najeriya.Malamin cewa yake yi; Don Allah ina so ku sanar da ni , wai shin wane shugaba ne ya fara aza harsashin ginin kasaitacciyar Ganuwar kasar chaina, wadda aka fi sani da suna (The great wall of Chaina) a Turance?

Amsa: A wajen shekara ta 220 kafin haihuwar Annabi Isa (AS), wani Sarki a Kasar Sin wato Chaina, wanda ake kira da suna (Qin shi Huang), ya yi kokarin hade dukkanin Al’ummar Kasar Sin a ma’tsayin Kasa daya al’umma daya. Kuma ana yi masa kirari da sarkin sarakunan kasar sin na farko, kuma sunan nasa “Qin” ko kuma “Ch’in” shine ya yi tasiri wajen samun asalin sunan na Kasar ta Sin wato Chaina.

Shi dai Sarki Qin, ya fara wannan aiki ne ta hanyar kirkirar hanyoyi na sarrafa kasa daban-daban, ana yin bulalluka kala-kala, kamar yadda muke da hanyoyi daban-daban na sarrafa kasa a kasar Hausa, wato irin yadda idan mutum ya tashi yin gini tun a zamanin da,za’a ga ana sarrafa kasa wajen yin su tubali,bulalluka da su daben makuba da dai sauransu, to haka shi ma Sarki Qin ya fara, inda ya fara gina yan kananan katangu akan iyakokin kasar Chaina, da nufin kare Kasar daga mahara. Daga baya sai yakara bunkasa wadannan katangu zuwa ganuwa, kai daga baya ma sai ya dauki mutane aiki na musamman, musamman ma dai mutanen kauye, domin ginin wannan ganuwa, a matsayin kasaitacciyar ganuwa.

Bayan rasuwar Sarki Qin, sauran sarakuna da suka maye gurbin sa, sun ci gaba da gina wannan ganuwa daga inda ya tsaya, tare da kara himma wajen ginin. Wato ko wanne Sarki ya zo, sai ya nunka akan kokarin da sarakunan baya suka yi.domin cin wannan buri na su, na gina wannan ganuwa.

Ita dai wannan ganuwa ta Kasar Sin, an shafe sama da shekaru 2000 kafin a ammala gininta, kuma bayan an kammala ta, tsayin nisan ganuwar ya kai kimanin tafiyar mil 4000 wato kilomita 6,700 kenan.Babban abin mamaki shine yadda aka tafi da ginin wannan ganuwa, domin kuwa ganuwa ce da aka tafiyar da ginin nata kamar ginin gada, wato tana da bangwaye dama da hagu, wato ma’ana a tsakiya akwai hanya wadda Al’umma suke ta kai-komo a cikin ta, wadda ta tashi tun daga babban birnin na kasar Sin wato Beijing zuwa wani gari mai suna Hadan.Baya ga wannan kuma, ita wannan ganuwa mai makon idan an tarar da kogi ayi gada a ci gaba da dora gini, a’a sai dai a bi da ginin ta jikin gabar kogin. Sannan kuma duk wani kwari ko kuma tsauni da wannan ganuwa ta tarar, tana bi ta kansa ne ta wuce, haka aka yi ta yi har aka kammala ta.