1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin garin Tasawa na jamhuriyar Nijar

Gazali Abdou TasawaMarch 2, 2016

Ana kyautata zaton an gina garin Tasawa a karshen karni na 16 zuwa farko na 17.Kuma kalmar sunan garin na Tasawa ta samo asali ne daga Tasa wato kwano. Akasarin al’ummar garin manoma ne da ‚yan kasuwa da kuma makera

https://p.dw.com/p/1I5cC
Karte Niger

Ana kyautata zaton an gina garin Tasawa a wajejan karshen karni na 16 zuwa farko na 17.Kuma kalmar sunan garin na Tasawa ta samo asali ne daga Tasa wato wani baho da ban ruwa. Akasarin al’ummar garin manoma ne da ‚yan kasuwa da kuma makera. Al’ummar Tazarawa ne suka fara kafa sarauta ta farko a garin na Tasawa wacce amma daga baya ta kasance a matsayin karamar masarauta da ke a karkashin ikon babbar masarauta ta Katsinawa wadanda suka zo daga baya. Yanzu haka dai Katsinawa da Tazarawa ko wane na da izinin tsayawa takarar neman sarautar garin na Tasawa a duk lokacin da aka zo zaben wani sabon sarki. Sarkin Tasawa na wannan lokaci shi ne sarki Mahamane Mansour Kane Maiguizo.

Sai a saurari cikakken shirin domin samun karin bayani.