1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya

November 1, 2010

Kasashen da su ka shirya gasar cin kofin kwallo ta duniya da kuma wanda su ka ci kofi daga farkon wasan zuwa yanzu.

https://p.dw.com/p/PvKb
Kofin kwallon kafa ta duniya

Ana shirya gasar cin kofin kwallon kafa a cikin ko wane shekaru hudu.Gasar cin kofi ta farko an tsara ta a shekara 1930 a kasar Yuruguai inda aka yi karon karshe tsakanin Yuruguai da Arjentina, Yuruguai ta samu nasara.

An yi karo na biyu a shekara 1934 a Italiya, inda Italiya ta dauki kofi bayan ta doke Chekoslovakiya.An yi gasa ta ukku a Faransa a shekara 1938 a wannan karo ma Italiya ta lashe kofin bayan ta cenye Hangri a karon karshe.

Daga wannan shekara sai aka dakatar da tsara gasar, saboda barkewar yakin duniya na biyu.Sai a shekara 1950 bayan kwanciyar hankali ta dawo a duniya sai Brazil ta shirya gasa ta hudu inda Yuruguai ta cenyi kofi.

An yi gasa ta biyar a kasar Switzerland a shekara 1954, karon farko Jamus ta Yamma ta zama zakara bayan ta lashe Hangri a karon karshe.

Shekaru hudu bayan wannan, kungiyoyin kwallo su ka hadu a kasar Swedin nan Brazil ta ci kofi.

A shekara 1962 Chili ta karbi bakuncin wassan, kuma Brazil ta gaji kanta da kanta a matsayin zakara kwallo ta shekara.

A shekara 1968 Birtaniya ta shirya gasar kuma ita ta ci kofi.

A shekara 1970 Mexiko ce ta shirya wasan kwallon na duniya kuma Brazil karo na ukku ta dauki kofi.

Jamus ta sake maimatawa daukar kofi karo na biyu a shekara 1974 a wasan da ta shirya.

Sai kuma 1978 Arjentina ta shirya gasar kuma ita ta ci kofi karo na farko.

A shekara hudu bayan hakan Spain ta shirya gasa kuma Itali ta kwaci kofi daga Arjentina.

Karo na 13 an shirya shi a Mexiko kuma Itali ta kwato kofi daga Arjentina.

A shekara 1990 Itali ta dauki bakunci gasar, kuma Jamus ta ci kofi bayan ta doke Arjentina.

A shekara 1994 an yi wasa a Amurika a nan Brazil karo na hudu ta samu nasara.

Faransa ta dauki yaunin gasa karo na 16, kuma a karon farko ita ta lashe kofi.

A shekara 2002 kasashen Koriya ta Kudu da Japan su ka hada karfi domin shirya gasar a nan ma Brazil ta dauko kofi.

Jamus ta dauki yaunin shirya gasa a shekara 2006, inda Itali ta samu nasara.

Sai kuma karo na karshe wanda a ka buga bana a Afirka ta Kudu, inda karon farko Spain ta samu nasara lashe kofi.

Brazil za ta shirya gasar cin kofin kwalon duniya nan da shekaru hudu masu zuwa.

Mawallafi Yahouza Sadissou Madobi

Edita Halima Balaraba Abbas