1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Golden Gate Bridge

Abba BashirMay 2, 2006

Bayani akan Golden Gate Bridge

https://p.dw.com/p/BvVU
Gadar Golden Gate Bridge
Gadar Golden Gate BridgeHoto: dpa

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon,ta fito ne daga hannun Malam Mujittapha Auwalu mazauni a birnin Omdurman dake Kasar Sudan.Malamin cewa ya yi , don Allah ina so ku bani tarihin hamshakiyar gadar nan ta birnin San Francisco dake Kasar Amurka,wadda ake kira da suna “Golden Gate Bridge’’ wadda kuma aka ce tana daga cikin Abubuwan ban mamaki da Injiniyoyin wannan zamanin sukayi a doron Kasa?

Amsa:To ita dai“Golden Gate Bridge’’wata hamshakiyar gada ce a Birnin San Francisco na Kasar Amurka, wadda ta hade garin na San Francisco da sauran garuruwan da ke tsallaken teku wadanda suke makotaka dashi. Har ila yau masana ilimin zane-zane wadanda da iliminsu na zane ne suka zana wannan gada ,da kuma injiniyoyi masana ilimin gine-gine wadanda suka gina ta ,suke tunkaho da ita a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka yi na gwaninta dakuma ban al’ajabi a wannan Duniya a Karni na 20.

Shekaru da dama dai gadar ta sha rike kambun zama gada wadda tafi dukkan gadoji irinta tsawo a Duniya, domin kuwa ita gada ce mai raga-raga wadda aka yita da wayoyi da kuma karafuna , bawai gada ce irin ta sumunti ba.

Kafin a kammala yin wannan gada a 1937, an dauka cewar wannan gada ce da baza a taba iya yin ta ba ,saboda irin mummunan yanayin da ake fuskanta a tekun da ake son yin gadar.Amma duk da irin wannan garari da ake gani a wannan kogi, sai gashi a tsakanin shekaru 4 zuwa 5 Allah da ikon sa ya ba da damar yin wannan gada, inda aka kashe kudi kimanin dalar Amurka Milliyan $35,000,000. Sai dai kuma mutane goma sha-daya (11) ne suka rasa rayukansu yayin aikin yin wannan gada

Kalar ruwan lema dai itace kalar da aka zaba ta zama kalar wannan gada domin ta saje da irin yanayin halittun da suke zagaye da wannan kogi. Har ilyau kuma akwai wasu igiyoyi na murdaddiyar wayar karfe guda biyu daga kowanne bangare na gadar wadanda suka daureta, wadanda kuma idan aka mikar da tsayinsuzai kai mil 80,000.Gadar dai har ila yau tana da dogwayen Kofofi guda biyu,wadda kowaccensu take da tsawon kafa 746 da kasa zuwa sama, sai kuma ginshikan da aka zuba musu kankaran sumunti a fandishon daya kai tsayin kafa 1,215 daga bakin ruwan Tekun.Kuma tsawon gadar gaba dayan ta yakai kafa 4,200.