1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin kamfanin dillancin labarai na AFP

Yusuf BalaJuly 18, 2016

An dai kafa wannan kamfani na dillancin labaran Faransa a shekarar 1944 bayan samun wata dama ta 'yantar da birnin Paris daga mamaya ta Jamusawa masu aikidar Nazi.

https://p.dw.com/p/1JOxe
Logo AFP
Alama ta kamfanin dillancin labaran Faransa na AFPHoto: Getty Images/AFP/F. Dufour

A shekarar 1940 lokacin da dakarun sojan Jamus suka mamayi birnin Paris sun karbe iko da ofishin yada labarai na Faransa inda aka maida shi kamfani mai zaman kansa mai suna Havas. A ranar 20 ga watan Agusta ne 1944 sojan kawance suka kwace birnin daga dakarun Jamus, hakan ya sanya rukunin 'yan jarida cikin 'yan fafutikar 'yantar da Paris suka karbi ofishin yada labaran na Faransa FIO inda anan ne suka fara fitar da labari na farko da sunan Agence France-Presse.

Wannan kamfanin dillancin labarai na AFP wato (Agence France-Presse) kamfani ne da ke dillancin labarai tsakanin kasa da kasa kuma yana da hedikwatarsa a birnin Paris na kasar Faransa.

Andai kafa wannan kamfani a wannan shekarar ta 1944 bayan samun wata dama ta 'yantar da birnin na Paris daga mamaya ta Jamusawa masu aikidar Nazi bayan yakin duniya na biyu, ya kuma kasance kamfanin dillancin labarai na uku mafi girma a duniya da ke bin bayan kamfanin dillancin labaran Associated Press (AP) da kamfanin dillancin labaran Reuters.

Bildergalerie 70 Jahre Kriegsende
Faransa a lokacin yakin duniya na biyuHoto: picture-alliance/dpa

Kamfanin na AFP na da ofisoshin yanki a birnin Nicosia na Jamhuriyar Cyprus da Montevideo na Yurugai da Hongkong da Washington D.C yana kuma da wasu ofisoshi watse a kasashe 150 na duniyar nan inda yake dillancin labaransa ga kafafan yada labarai a harsunan Faransa da Ingilishi da Arabic da yaran Portuguese da Sapaniyanci da Jamusanci.

Shugaban wannan kamfani dai a yanzu shi ne Emmanuel Hoog sannan daraktar yada labarai kuma ita ce Michèle Léridon.

Akwai dai irin wadannan kamfanoni da dama a kasashen duniya wadanda ke da wakilai da aikinsu shi ne su kutsa duk wani lungu da sako na duniya dan neman labarai dan siyarwa ga wasu kafofi na yada labarai. Alal misali kamfanin dillancin labarai na Jamus DPA na da ma'aikata 1,200 watse a kasashe 90 a fadin duniya yana kuma yada labaransa a harsunan Jamus da Ingilishi da harshen Spaniya da Arabic kuma hanyoyin bada labaran kamfanin sun hadar da wanda ake gurzawa da Rediyo da talabijin kai harma da wayoyin tafi da gidanka da intanet.

Timeline 2er Weltkrieg Hitler Tod
Dakarun soja a lokacin yakin duniya na biyu na karatun jaridaHoto: picture alliance/dpa/Everett Colle

A kwai dai irin wadannan kamfanoni da ke dillancin labaran a kasashen duniya daban-daban ya danganta da inda wata kafa ta yada labarai ke muradi kamar misali ta nan DW wacce ke da kafofi da dama da labarai ke zuwa mata. Wasu karin fitattun da ake jinsu sun hadar da kamfanin dillancin labaran Xinhua na China kenan ko IRNA ko ISNA a Iran da Kyodo News Japan da Press Trust of India da NAN a Najeriya da Anadolu a Turkiyya Yonhap News Agency Koriya ta Kudu. Ga sunan dai da dama a fadin duniya, sukan samo labarai da editocinsu ke aiki a kansu kafin su fitar da su wata kafa ta siya dan watsawa.