1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Kasar Haiti

Abba BashirOctober 4, 2005

Takaitaccen Tarihin Kasar Haiti

https://p.dw.com/p/BwXM
Bikin Al'ada a Haiti
Bikin Al'ada a HaitiHoto: AP

Masu sauraron mu barkan mu da sake saduwa cikin wani sabon shirin na amsoshin takardun ku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya-Fatawar mu ta wannan makon ta fito ne daga hannun mai sauraron mu a yau da kulum Yusuf M. Jada mazauni a birnin Port Harcourt dake tarayyar Nigeria,mai sauraron namu so yake yi mu bashi tarihin kasar Haiti.

Amsa-Kasar Haiti dai ta kasance cikin jerin kasashen Caribbean da Allah ya horewa albarkatun ruwa, Kasar dai tana kan tsibiri ne,wacce kuma keda tsaunuka da yanayi na kasa mai albarka.

A farkon kafuwar wanan kasa dai Christoper Colubus ne ya sauka a kan wannan tsibri a watan Disamban 1492,koda yake a wanan lokacin ana kiran tsibrin na Haiti da sunan tsibirin Hispanola.

Daga baya kuma kabilun Arwaka da suka fito daga India suka mamaye wannan tsibiri,kafin kuma ’yan mulkin malakar Spain su fatattaki ’yan kabilar ta Arwaks daga kan tsibirin na Haiti.

Kasashen Birtaniya da faransa da Spain sun mamaye tsibirin na Haiti,dai kuma a tsakiyar karni na 17 ne tsibirin na Haiti ya koma karkashin mallakar kasar faransa.

A lokacin mulkin malakar Faransa,tsirin na Haiti ya sami cigaba ta fanoni da dama,inda har ma ya kai ana bukatar kayayyakin da ake sarrafawa a kasar a kasuwannin nahiyar Turai.

Tsibirin dai na Haiti,Allah ya hore masa arzikin Cocoa,Auduga,Coffe da kuma rake,to sai dai kuma irin tsananin bukatar da ake yiwa irin wadanan albarkatu ya sanya ana bukatar karin maaikata don su gudanar da aiyuka na kodago a gonakin Cocoa,rake,auduga da dai sauran su.

A sabili da haka ne ’yan mulkin mallakar faransa suka ga cewar babu wata mafita illa su nufi yammacin Africa da nufin sayo bayi da zasu rika yi musu aiyuka a gonakin rake da dai sauran su,saboda haka a iya cewa bakaken fatar tsirin Haiti sun fito ne daga yammacin Africa.

A shekara ta 1780 kasar Haiti ta zamanto,daya daga cikin yankuna na kasahen Duniya dake da arziki.

’Yan mulkin malakar faransa sun shiga cinikin bayi daga nahiyar Africa ne da nufin hakan ya taimaka wajen cimma manufar cigaban tattalin arziki a tsibirin na Haiti,to sai dai kuma ci gaba da sayo bayi daga Africa ya haifar wa da kasar ta faransa matsaloli a fuskar cigaban kasar ta Haiti,ta la’akari da irin azabtarwar data rika yiwa bayin data sayo daga nahiyar Africa.

A shekara ta 1780,an gudanar da boren kin jinin cinikin bayin da turawan mulkin mallakar Faransa ke yi a tsibirin na Haiti,inda hakan ya sanya aka kifar da gwamnatin Napoleon kafin kuma a shekara ta 1804 tsibirin na Haiti ya sami yancin kansa,inda janar Dessalines ya baiyana kansa a matsayin shugaban kasa.

To sai dai kuma salon mulkin kama karya da ya rika shimfidawa a tsibirin na Haiti,ya sanya Henri Chiristophe ya sa a yiwa Napoleon din kisan gilla.Cheristophe ya dare kann karagar mulkin arewacin tsibirin na Haiti.

Kasar dai ta Haiti na zaman tsohuwar kasa ta bakar fata a duniya,kuma ’yan asalin kasar ta Haiti sun taka muhimiyar rawa wajen juyin juya halin da ya faru a Amurka,tare kuma da taimakawa wajen ganin kasahen Latin Amurka sun sami yancin kan su.

Bayan da kasar Haiti ta ta sami yancin kanta daga turawan mulkin malakar faransa,ta rabu kashi biyu izuwa yankin arewaci da kuma kudanci,to sai dai kuma sun sake hadewa a shekara ta 1820.

Bayan shekaru biyu ne dai Haiti ta mayaye Santo Domingo,yankin gabashi da ke magana da harshen Spanish na Hisponiolaa.

A shekara ta 1844 ne kuma yakin na Santo Domingo ya balle daga kasar Haiti,ya zama jamhuriyar Dominican.

An dai fuskanci matsaloli masu yawa na rudanin siyasa da tattalin arziki a tsibrin na Haiti,inda har ma sai da Amurka ta aika dakarunta na kiyaye zaman lafiya a shekara ta 1915 da nufin ganin an sami tabbataccen zaman lafiya a haiti,saboda sai da aka sami sauyi na gwamnati har 22 a tsakanin 1843 zuwa 1915,kuma dakarun na Amurka basu fice daga cikin kasar ta haiti ba sai a shekara ta 1934,a lokacin da zababbiyar gwamnati ta bukaci ficewar sojin na Amurka daga kan tsibirin na Haiti.

Muna fata mai sauraron namu ya gamsu da wannan amsa.