1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Kungiyar Kwallon Kafa ta Leicester City da ke Ingila

Aliyu AbdullahiMay 23, 2016

Kungiyar kwallon kafa ta Leicester city, ta kasance daya daga cikin kulab-lukan dake karawa, a gasar Premier League na kasar Ingila, ita ce a karon farko, ta lashe gasar Premier League na Ingila.

https://p.dw.com/p/1Iszu
Leicester City Spieler
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Super

Kungiyar kwallon kafa ta Leicester city dai, na daya daga cikin kulab-lukan dake karawa, a gasar Premier League na kasar Ingila. Wadda aka kafa ta, fiye da shekaru 100 da suka gabata. Kuma a karon farko, ta lashe gasar premier league din na Ingila, a kakar wasanni ta 2015/2016 tare da sabon mai horar da kungiyar na Leicester city, dan kasar Italia, Claudio Ranieri, wanda kuma hakan ya basu damar shiga gasar zakarun kulab-lukan nahiyar Turai, wato UEFA Champions League na shekarar 2016/2017. Gasar da kulab-lukan Manchester United, Liverpool da Chelsea, ba za su samu damar shiga ba.

Kungiyar kwallon kafa ta Leicester city, ta kafu ne a shekarar 1884 a matsayin Leicester Fosse, kasancewar tana doka wasanta ne, a filin Fosse Road, kafin ta koma yin wasa a Filbert Street a shekarar 1890. Leicester city ta shiga gasar Midland 1891, wanda a karawarta na farko a gasar league, ta sha kashi ne da ci, 4 da 3 a hannun kungiyar kwallon kafa ta Grimsby. Babban nasarar da kungiyar ta yi kuwa wannan kakar wasannin shine baiwa kungiyar Rotherham kashi da ci 13, da nema.

Kungiyar ta samu canjin suna ne, daga Leicester Fosse, zuwa Leicester city ,a shekarar 1919-1939, wato bayan da yankin ´Borough of Leicester, ya samu matsayin kasancewa cikakken birni, kuma an sake zabar Kungiyar ta Leicester city dan shiga gasar league, 1915, bayan da aka dakatar ta gasar league din baki daya, har na tsohon shekaru hudu, sakamakon rashin kudin gudanarwa.

A shekarar 1925, kungiyar ce ta lashe gasar ´yan rukuni na II, karkashin jagorancin mai horar da kungiyar na wannan lokaci, Peter Hogde. A cikin ´yan kwallon da kocin ya kawo kungiyar, har da Arthur Chandler, daya daga cikin sanannun ´yan kwallo a birnin, a wannan lokaci, wanda yayi nasarar jefa kwallaye har 273 a tarihin kulub din, tsakanin 1923 zuwa 1935, sai Adam Black wanda shi kuma yayi nasarar zira kwallaye 528.

England Leicester King Power Stadium Logo Fahne
Hoto: Imago/Action Plus

Frank Mc Lintock ya kasaance fitaccen dan kwallon kungiyar na Leicester city, wanda yayi wasa a kulub din, har na kakannin wasa bakwai, cikin nasara, tsakanin 1957 zuwa 1965, wanda kuma ya gaji Jimmy Bloomfield a shekara ta 1977, kasancewar ya jagoranci kungiyar ga fadawa gasar kungiyoyin kasa, wato relegation kenan, a kakar wasanni na 1977/1978 , bayan kuma da ya mika takardar ajiye aiki, ana kallonsa a matsayin mai horarwa mafi koma baya a tarihin kungiyar. Jock Wallace shine ya karbe shi idan ya dawo da martabar jerin kwaca-kwacai, ´yan asalin kasar SCOTLAND, bayan da ya dawo da su cikin gasar ´yan rukuni na I, 1980, duk da dai Wallace, ya kasa ketarawa da kungiyar Leicester city zuwa gasar rukuni na gabaI, amma a wannan shekarar ce ya jagorance su, ga kaiwa wasan kusa da na karshe a gasar FA cup na kasar ta Ingila, kuma na farko a tarihin kungiyar, a 1982. A karkashin mai horaswa Wallace, daya daga cikin sanannun ´yan wasan yankin Leicester mai suna Gary Lineker, ya samu shiga cikin jerin fitattun ´yan wasan kungiyar. Kuma sabon mai horaswan Leicester city, ya kasance Gordon Milne, wanda ya samu karin girma a shekara ta 1983. Lineker, ya jagoranci Leicester city wajen rike matsayinsu a rukuni na farko, amma sai aka sai da shi, ga kungiyar kwallon kafa ta Everton, a 1985.

Brian Little, wanda ya ketaro da Kungiyar Darlington F.C daga rukunin Conference, zuwa rukuni na III, da kuma samun karin girma akai-akai, shine ya samu zama sabon mai horaswa na kungiyar ta Leicester city, inda bayan sun doke Kungiyar Cambridge United da ci 6 da 1, a wasan kusa da na karshe na wasannin share fage, suka samu kasa shiga gasar premier league, bayan suma sun sha kashi a hannun Blackburn Rovers, da kwallo daya mai ban haushi, wanda kuma tsohon dan wasan kungiyar Leicester ne ya zira shi, mai suna Mike Newell. Kwallon da aka zira musu ta hanyar ´bugun daga kai sai mai tsaron gida´, wanda dan wasa mai suna Steve Walsh ne ya janyo shi, kuma abin da ya janyo mishi tsana daga masu goyon bayan kungiyara, saidai dagaa baya ya sake ratafa musu hannu a shekarar gaba. Leicester city dai, ta fafata sosai kafin su sami shiga gasar premier league, bayan da suka doke kungiyar Derby County F.C da ci 2 da 1,a shekarar 1993-1994.

A shekarar 1996-2000, Leicester city, sun tabbatar da zamansu a gasar premiership, rukuni na biyu, bayan da suka kasance a jerin kungiyoyi goma na rukunin farko a gasar ta premiership, har tsahon shekaru hudu. O'Neill shine mai horaswarsu, na farko, daya ciwo musu kofi, a cikin shekaru 26, tare da lashe kofunan league guda biyu.

Fußball Manchester United gegen Leicester City Barclays Premier League
Hoto: Getty Images/L. Griffiths

Leicester city, sun samu shiga gasar wadanda suka lashe kofin gasar cikin gida, wato European Cup Winners, a 1997-1998 da kuma 2000-2001, wato sun samu damar shiga gasar nahiyar turai kenan tun karon farko a 1961-1962. O'Neill, ya kasance mai horaswa mafi farin jin da nasara, a tarihin kungiyar, a watan Afrilu, na 2000 ne, kungiyar ta karbi Pound dubu goma sha daya 11, a hannu kungiyar Liverpool dan saye dan was an gaba wato Emile Heskey, daga kulub din.

Leicester city, sun fara wasan farko a gasar premier league ne a 2004, da yin canjaras har sau biyu, a wasanninsu guda uku na farko. Sun samu nasararsu ta farko ne, inda suka doke takwarasu, wato kungiyar Stoke city da ci daya tilo, sannan a kakar wasannin 2014/201, sun baiwa kungiyar Man Utd. Kashi da ci 5 da 3,karkashin jagoraanci Louis Van Gaal, abin da ya sakasu a matsayi na bakwai, a gasar na premier. Ko da yake, sun kare kakar ne a matsayi na goma sha hudu (14).

A kakar wasanni na 2015/2016, kungiyar Leicester city, ta kasance ne a karshen rukunin kungiyoyin da ke doka wasannin premier league, inda kowa yake ganin kamar ba za ta iya ci gaba da zama a gasar premier league din ba, kamar su William Hill, wanda ke cewa baya tunanin kungiyar ta Leicester za ta kai ga iya lashe gasar a wani yanayi da ba a taba samun irinsa ba.

Karkashin jagorancin sabon kocin kungiyar, Claudio Ranieri, kungiyar ta fara wasanninta da karsashi da sa'a da kuma karfin gwiwa, inda ta sha kashi sau daya kacal, a wasanni 15 na fari, wanda ya basu damar darewa kan taburin jagoranci a gasar, a gaban kungiyar Arsenal, da Manchester city, da kuma Manchester United. Dan wasan gaba na kungiyar mai suna Jamie Vardy, ya doke tarihin da Ruud Van Nistelrooy ya kafa 2003, na yawan jefa kwala-kwalai, sanda ya kewa Man Utd. Wasa. Wato a december , 2014 sun kasance a karshen tebur, amma a december, 2015 su ne, a kan tebur.

Fußball Leicester City Trainer Claudio Ranieri
Hoto: Getty Images/M. Regan

A February, 2016, sun kara azama, inda suka doke kungiyar Man City da ci 3 da1 har gida, kuma dai, abin mamaki, kungiyar Tottenham ne, ke binsu sau da kafa, har a karshe kungiyar Arsenal ta ture su, dan kasancewa a matsayi na biyu, inda ita kungiyar Tottenham din ta koma matsayi na uku, da Man City a matsayi na hudu, Man Utd, kuwa da ta zo na biyar, ba za ta samu shiga gasar UEFA Champions league. Leicester dai, a karo na farko a tarihi, za a fafata da ita a gasar zakaru na nahiyar turai, wato UEFA Champion League.