1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Marigayi Sir,Ahmadu Bello.

Abba BashirAugust 15, 2005

Tarihin Marigayi Sir,Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.

https://p.dw.com/p/BwXT
Tutar Nigeria
Tutar Nigeria

Masu sauraron mu asalamu alaikum barkan mu da sake saduwa cikin wani sabon shirin na amsoshin takardun ku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya: fatawar farko a cikin shirin ta fito ne daga hanun Sadikou Almou inkiya shugaban hukumar gidan Gona Zinder BP.149 Zinder jamhuriyar Niger,mai sauraron namu cewa yayi mu bashi tarihin gwarzon gwarzaye marigayi Sir Ahmadu Bello tsohon Primiyan jihar Arewa a Nigeria.

Amsa: An haifi marigayi Sir Ahmadu Bello a garin Rabah dake cikin lardin Sakkwato a shekara ta 1910,kuma dan sarauta ne jinin shehu dan Fodio,wanda ya kafa daular fulani.Da yake shekara 16 da haihuwa bayan ya sami iliminsa na makarantar lardi ta Sakkwato,sai wuce zuwa kwalejin horon malamai ta katsina,inda yayi karatu daga 1926 zuwa 1931.A kwalejen ta Katsina ya rike mukamin mai unguwa,kuma yayi kyaftin na yan wasan Fives.Bayan da ya fita a matsayin malamin makaranta,ya koyar a makaranatr Middile ta Skkwato daga 1931 zuwa 1938.Daga nan ne kuma aka nada shi Sardaunan Sakkwato,watau mai baiwa sarkin musulmi shawara akan harkokin siyasa.

Daga nan sai aka danka masa shugabancin yakin gabas na Sakkwato,wato Gusau inda hakimai goma sha hudu daga cikin arba’in da bakwai na Sakkwato ke karkashinsa.A 1944 ya koma Sakkwato a mukamin baban mai bayar da shawara ga sarkin musulmi,

shine a lokacin yake duba gundumomi,yake kuma duba sasan aiki na NA.A shekara ta 1948,ya kai ziyarar aiki Ingila inda ya sauka a gidan abokai,kuma suka zagaya da shi kasar,ya kuma zauna da su yana halartar kwas akan mulkin kanan hukumomi.A shekara ta 1949 marigayi sarduna ya sami zuwa majalisar dokoki ta jihar arewa,yana kuma daga cikin mutum na uku da aka zaba cikin kwamitin da ya rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasa.

An nada shi firimiyan Najeriya ta arewa a shekarar 1954.kuma ya riki wannan mukami har tsawon shekaru goma-sha-daya,lokacin da aka kashe shi a yunkirin juyin malkin soja na farko a kasar ta Najeriya.

Kashe wannan bawan Allah da Allah yayiwa baiwa ta basira da tunani da kuma hangen nesa,an yi shi ne da nufin raba shi da mulkin Najeriya ta arewa.To haka kuwa al'amarin ya kasance,domin kuwa kasheshin da aka yi a ranar 15 ga watan janairun 1966 a yunkurin juyin mulkin soja na farko a Najeriya,shine ya kawo karshen tsarin mulkin jamhuriya ta farko a wannan kasa.

Sojan da ya kashe shi kuwa ya haska Fitina ne don ya gane sardauna,a lokacin sarduna na kalonsa ya harbe shi har lahira,ya kuma harbe uwargidansa da suke tare Habsatu,koda yake an harbe sarduna amman kuma duka da haka yana tsaye bai fadi ba,jikinsa duk jini,a wanan lokacin ne kuma sallam ta taba shi,ya gane cewa sarduna ya gamu da ajalinsa,

Ba’a dai taba sauran matan Marigayi sardauna ba,in banda uwarginsa da aka harbe su tare.

Sardauna yasan cewa za’a yi juyin mulki a wanan daren,don haka ne ya umarci kowa ya bar gidan da suke zaune na birnin Kaduna.

Tarihi ya nuna cewa Alh.Aliyu magajin garin Sakkwato ne ya sanarda sarkin musulmi rasuwar sardauna wanda daga bisani ne sarkin musulmi ya yarda a yi jana’izarsa tare da matarsa Hafsatu.

Marigayi shiekh Abubakar Gumi ne ya shugabanci Sallar jana’izar Marigayi Sardauna Sir Ahmadu Bello.

Muna fata Sidikou Almou mazuni a Zinder cikin jamhuriyar Niger ya gamsu da wanan amsa.