1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin rayuwar marigayi sarki Fahad Bin Abdul-Aziz na saudia

ibrahim saniAugust 1, 2005

Aiyyukan sarki Fahad da kuma tarihin sa yana gadon sarautar Saudi Arabia

https://p.dw.com/p/Bvai
Hoto: AP

To da farko dai sarki Fahd Bin Abdul-aziz, sarki na biyar a jerin sarautar kasa mai tsarki an haife shine a shekara ta 1921, ya kuma shafe shekaru ashirin yana gadon sarautar mulki kafin rasuwar sa a yau litinin yana da shekaru 83.

Tun kafin Sarki Fahad ya zamo sarki ya kasance mai fada aji a lokacin mulkin sarki Khaled da zamanin mulkin sa ya kare a shekara ta 1982.

Kafin zaman sa sarkin Makka da yawa daga cikin alummar kasar na shakkun yadda shugabancin sa zai kasance a matsayin sarki bisa halayyar sa data yi kama da kasashen yamma.

Wannan hasashe da alummar kasa keyi masa a wancan lokaci ya kasance gaskiya, domin kuwa a lokacin tsawon mulkin sa na shekaru ashirin da sukla gabata, sarki Fahad ya kulla dangantaka ta kut da kut da mahukuntan kasar Amurka.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa sarki Fahad ya dare wannan kujera ne mai alfama ta kasar ta saudi arabia a shekara ta 1982, wanda a tsawon mulkin sa kasar ta samu fita daga kangin na sahara da talauci izuwa daya daga cikin kasashe dake da karfin tattalin arziki a duniya.

Sarki Fahad a lokacin yana rike da madafun iko, ya kirkiro wasu sabbin sauye sauye a tsarin mulkin kasar ta hanyar nada kwamitin shura mai bada shawara daya kunshi mutum sittin. Ya zuwa yanzu dai wannan majalisa ta kunshi a kalla mutane 150, to amma wadanda suke shiga cikin ta sun kasance zababbu ne daga bangaren masarautar kasar.

A kuma sakamakon matsi daga kasashen ketare, musanmamma Amurka, kasar ta Saudia ta aiwatar da wasu sabbin sauye sauye a cikin harkokin siyasar kasar inda a karon farko aka gudanar da zabubbuka na kana nan hukumomi.

A lokacin mulkin sa, sarki Fahad yayi amfani da makudan kudaden da kasar take samu daga danyan man fetur wajen tallafawa gwamnatin Saddam Hussain ta iraqi yakar kasar iran. To amma a yayin da Saddam Hussain ya afkawa da kasar Kuwait da yaki sai sarki Fahad ya gayyaci dakarun sojin Amurka izuwa kasa mai tsarkin don ceto wannan kasa ta Kuwait a shekara ta 1991.

Daukar wannan mataki na kyale wadanda ba musulmai ba a kalla rabin miliyan shigowa kasar asalin musulunci kuma kasa mai tsarki ya haifar da tsana da tsangwama ga gwamnatin sa daga da yawa daga cikin alummar kasar, musanmamma ga mai son kawo sauyi, wato Usama Bin Laden.

Ba tare da daukar wani tsawon lokaci ba sai Usama bin Laden ya juyawa wannan gwamnati ta Fahad baya tare da abokanan sa wato Amurkawa. Shekaru goma baya sai Usama Bin Laden tare da taimakon kungiyyarsa wato Alqeeda ya kaddamar da harin nan na sha daya ga watan satumba, wanda ya girgiza Amurka da kuma duniya baki daya.

Duk da dangantaka mai gwabi gwabi dake akwai a tsakanin Amurka da kasar ta Saudi Arabia, wannan hari na sha daya ga watan satumba ya haifar da nakasu ga wannan dangantaka data dade tana wanzuwa a tsakanin kasashen biyu.

Bayan wannan ta faru ne kuma a shekara ta 2003, kungiyyar ta Alqeeda ta kaddamar da kamfe na hare hare a kasar ta Saudi Arabia, musanmamma akan baki yan kasashen ketare da jamian tsaro da kuma rijiyoyin hakar man fetur na kasar.

A dai dai lokacin da wadan nan abubuwa ke faruwa, sai sarki Fahad ya gamu da matsananciyar rashin lafiya ta mutuwar rabin jiki a shekara ta 1995.

Bisa halin mutu kwakwai rai kwakwai da sarki Fahad ya samu kansa a ciki ala tilas ya mika tafiyar da ragamar mulki ga dan uwan sa wato Yarima Abdullah.

Sanin rashin tabbas game da rashin lafiyar da sarkin yake fama da ita ya haifar da kace nace a masarautar kasar a tsakanin yarima Abdullah wanda dane ga dan uwan sarkin da kuma yan uwan sarki na kut da kut, wato Ministan maikatar tsaro da kuma na cikin gida game da neman madafun ikon kasar idan rai yayi halin sa.

Jim kadan dai bayan da masarautar kasar ta bayar da labarin rasuwar sarkin a yau litinin nan take kuma ta bayar da sanarwar nada yarima Abdullah a matsayin sabon sarki na kasar ta Saudi Arabia.

Da yawa daga cikin alummar kasar da kuma ma na kasashen ketare na ganin cewa da wuya ne a samu sauyi game da matakan kasashen ketare a gwamnatance, bisa la,akari da cewa Yarima Abdullah ya kasance mai tafiyar da ragamar mulkin kasar tun kafin rasuwar tsohon sarkin.