1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Roch Kaboré na Burkina Faso

Yusuf BalaDecember 7, 2015

A shekarar 1984 Kabore ya na da shekaru 27 ya zama Darakta Janar na bankin na BIB ya rike wannan mukami tsawon shekaru biyar tun daga shekarar 1984 zuwa 1989.

https://p.dw.com/p/1HIc5
Burkina Faso Präsidentschaftswahlen Roch Marc Christian Kabore
Roch Marc Christian Kabore a lokacin da yake kada kuri'aHoto: DW/K. Gänsler

Shi dai Roch Marc Christian Kaboré an haife shi a ranar 25 ga watan Afrilu na shekarar 1957 a birnin Ouagadougou babban birnin kasar ta Burkina Faso, ya yi makarantar firamare tsakanin shekarar 1962 zuwa 1968 daga nan ne ya tafi kwalejin Saint Jean Baptiste wata fitacciyar makaranta a birnin Ouagadougou inda, ya yi karatu tsakanin shekarar 1968 zuwa 1975, bayan kammala karatun sakandare ya tafi jami'a inda ya yi karatu da samun takardar digiri a fannin huldar kasuwanci a jami'ar Dijon a shekarar 1979 sannan digiri na biyu a shekarar 1980.

Kabore ya yi aiki a bankin kasa da kasa na Burkina Faso wato BIB inda ya kai ga matakin jagorantar wannan banki, A shekarar 1984 Kabore ya na da shekaru 27 ya zama Darakta Janar na bankin na BIB ya rike wannan mukami tsawon shekaru biyar tun daga shekarar 1984 zuwa 1989 wanda a wannan lokaci ya shiga harkokin siyasa.

Ya rike mukami a gwamnatin kasar ta Burkina Faso inda ya zama minista sannan ya zama mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa har ma dai ya kai ga mukamin Firaminista a shekarar 1994 . A lokacin da aka kafa jam'iyyar CDC a farkon watan Fabrairu na shekarar 1996 Mista Kabore ya sauka daga mukaminsa na Firaminista, sannan ya zama mataimakin shugaban kasa da mai ba wa shugaban shawara a jam'iyya mai mulki.

Burkina Faso Wahl in Ouagadougou
Masu muranar nasarar zabe a OuagadougouHoto: picture-alliance/AP Photo/T. Renaut

A ranar 6 ga watan Yuni na shekarar 2002 an zabe shi a matsayin shugaban majalisar dokokin Burkina Faso inda ya gaji Melegue Maurice Traore. Ya dai rike makamai da dama da suka hadar da ministan sadarwa da sufuri da sakataren jam'iyyar CDP a shekarar 2003 da ma zama shugaban jam'iyyar a shekarar 2003.

Mista Kabore tare da wasu jiaga-jigai na jam'iyyar ta CDP sun bayyana ficewa daga jam'iyyar ta CDP a ranar 6 ga watan Janairu a shekarar 2014 in da suka ce sun fice ne saboda dalilan cewa yadda jam'iyyar take tafiyar da lamuranta basa tafiya da tsari irin na dimokradiya a watan Janairu na 2014 an kafa sabuwar jam'iyya ta Peoples Movement for Progress wacce ta zama babar jam'iyyar adawa.

Burkina Faso Präsidentschaftswahlen Kandidaten Kabore und Diabre
Kabore da DiabreHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo/picture alliance/AA/Olympia de Maismont

A zaben da aka yi a ranar 29 ga watan Nuwamba na wannan shekara , Mista Kabore ya samu nasara tun a zagayen farko inda ya samu sama da kashi 53 cikin dari na kuri'un da aka kada wanda yazo na biyu, Zeprini Diabre ya samu sama da kashi 29 cikin dari na kuri'un da aka kada a wannan zaben kasar ta Burkina Faso da ya kafa tarihi.