1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin samuwar firinji

April 23, 2009

Taƙaitaccen bayani game da samuwar firinji da kuma wanda ya fara ƙirƙirar firinji na zamani.

https://p.dw.com/p/Hch0
FirinjiHoto: BilderBox

Tambaya: Fatawar farko a shirin namu, ta fito daga hannun malama Na'ima Isma'ila Habib daga Makkatul Mukarramah. Malamar cewa ta yi; Deutsche Welle, ku ba ni tarihin samuwar firinji, da kuma mutumin da ya ƙirƙiri firinji a duniya?

Amsa: Firinji dai wata na'ura ce mai daɗaɗɗen tarihi da ake amfani da ita wajen ajiye kayayyakin abinci, ko maganin da yanayin zafi kan iya lahantawa. Kuma a kan yi ajiyar ruwa a cikin sa domin ya sanyaya. Amma dai ko kafin ƙirƙirar firinji, an yi amannar cewa, mutanen da can na da dabaru irin nasu na adana abinci ba tare da ya lalace ba. Kuma irin waɗannan dabaru ne sannu a hankali aka inganta, har firinji ya samu da yanzu ake amfani da shi a gidaje da kuma ɗakunan girki irin na zamani.

Mutanen da, kamar yadda bincike ya nuna sukan sami wuri mai sanyi kamar gaɓar kogi su adana abinci don kar ya lalace, ko kuma su haƙa ƙarƙashin ƙasa a wuri mai dausayi. A ƙasahen da tsabar yanayin hunturu kan sanya zubar dusar ƙanƙara kuwa, tun kafin ƙarni na 19 mutane kan sari dunƙulen ƙanƙarar su saka cikin wani ɗan akwatin katako, kana su jera nau'o'in abincin da ke buƙatar sanyi don kar su lalace.

Irin waɗannan dabaru ne dai masu bincike irin su Dr. William Cullen da Dr. John Goorie da Michael Faraday, suka gina fasahar su akai, tun a farkon ƙarni na 18 da tunanin samar da wata na'urar sanyi da tafi wancan akwatin katako na kankara inganci.

Waɗannan dabarun masu bincike ne dai wani Bajamushe mai suna Injiniya Carl Von Linden, ya tattara a shekarar 1876, ya ƙera firinji na farko a duniyar nan. Inda Injiniya Linden ya ci gaba da bincike tare da inganta wannan fasaha tasa ta ƙera firinji. Sauran masana da kuma injiniyoyi na wannan zamani kuma suka kwaikwayi fasahar Injiniya Linden suka ci gaba da ƙera firinji.

Ya zuwa shekarar 1920 dai, an samu kafuwar kamfanoni fiye da 200 da suke ƙera firinji iri daban-daban a wannan duniya, bisa dogaro da fasahar Injiniya Linden, wanda aka yi ittifaƙin cewar shi ne ya fara ƙirkirar firinji har 'yan baya suka runguma.

Yau dai an wayi gari cewar, firinji ya zama ruwan dare game duniya. Ya kuma zama wani sinadari na tafiyar da rayuwa, kama daga amfani da shi wurin adana abinci zuwa samar da ƙanƙara, kai har ma da killace magani walau na Bature ko kuma na gargajiya, domin kare shi daga lalacewa.

Mawallafi: Abba Bashir

Edita: Umaru Aliyu