1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Shugaban Kasar Sudan Umar el- Bashir

Abba BashirNovember 17, 2005

Takaitaccen Tarihin Umar el-Bashir

https://p.dw.com/p/BvVj
Omer el Bashir da Marigayi John Garang
Omer el Bashir da Marigayi John GarangHoto: AP

Masu sauraron mu assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa cikin wani sabon shirin na amsoshin takardun ku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya-Fatawar mu ta wannan makon ta fito ne daga hanun mai sauraron mu a yau da kulum Alh.Idi Ibrahim B.P.1313 mazani a birnin Ndjamena na kasar Chadi,mai sauraron namu cewa na rubuto muku wanan takarda ne,saboda ku bani cikaken tarihin shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir.

Amsa-An haifi shugaban kasar ta Sudan Omar al-Hassan Ahmad Bashir a shekara ta 1945 a garin Hoshe Bannaga mai tazarar kilomita 100 daga yankin arewa maso gabashin birnin Khartoum.

Ya kuma fara karatunsa na babar makarantar Middile ta Ahlia dake garin Shendi,daga nan ne kuma mahaifansa suka yi kaura zuwa birnin Khartoum a chan din kuma ya kama iliminsa na sakandre.Shugaban kasar dai ta Sudan ya cigaba da daukar nauyin karatunsa ne da irin taimakon da yake samu na kudade daga mahaifansa da kuma dan abinda yake samu a lokacin da yayi aiki a wani garejin gayaran motoci a birnin na Khartoum.

Bayan da shugaban kasar ta Sudan Omar al-Bashir ya kamala iliminsa na sakandre,ya shiga makarantar horarsa da sojin sama ta kasar Sudan,inda har ya sami horo na tuka jirgin sama.

A nan din ne kuma sami baban mukami a tskanin dakarun saman kasar Sudan,kafibn kuma daga bisani ya zama shugaban Brigade din sojojin kasa na kasar Sudan.

Omar Hassan Ahmad al-Bashir shugaban kasar Sudan mai ci a yanzu,sami manyan degrori biyu na Masters a fanin kimiyar aiyukan soji,a kwalegen horars da kumandojin soji ta Sudan da kuma kasar Malaysia.

Haka zalika al-Bashir ya halarci kwalejin horas da soji ta birnin Cairo,inda har ya shiga cikin sojin kasar Masar,a lokacin da masar din ta yi yaki da Isra’ila a shekara ta 1973.

A shekara ta 1988,an nada Omar al-Bashir kann mukamin kumandan Birgde ta 8 ta sojin Sudan a yankin kudancin Sudan,inda aka dora masa alhakin yaki da yan tawayen kudancin Sudan.A watan Yuni na 1988 shida wasu manyan hafsoshin soji,sun hambarar da zababiyar gwamnatin hadin kann kasa,karkashin shugabancin Sadiq Al-Mahdi.

Manufofin gwamnatin Al-Bashir game da dabaka tsarin shariar musulunci a Sudan,ta haifar masa da rashin fahimtar juna tsakaninsa da alumomin kudancin Sudan da mafi yawan su suka kasance kiristoci,wanan dalili ne ma ya kara rura wutar fadan yan tawayen kudancin Sudan.

A lokacin da Janar al-Bashir ya karbi ragamar mulkin Sudan ta hanyar juyin mulki irin na soji a ranar 30 ga watan Yunin 1989,an rika tababar cewa anya al-Bashir zai iya rike ragamar mulkin kasar ta Sudan da yakin basasa ya dai daita.A lokacin da al-Bashir ya karbi ragamar mulkin Sudan yana da shekaru 42 a duniya,kuma shine din ke zaman jami’in soji na farko da suka taka muhimiyar rawa wajen kai farmaki kann alumomin kudancin Sudan.

Kasar dai ta Sudan an kasata kashi biyu,tsakanin larabawa musulmi na arewaci da kuma kiristoci dake zaune a kudancin na Sudan.

Kungiyar yan tawayen Sudan ta SPLA ta fara yakin neman yanci ne a shekara ta 1983,kuma tun daga wanan lokacin ne,kafin ma mulkin al-Bashir gwamnatocin da suka gabata,sun yi yaki da yan tawayen kudancin Sudan.

Kungiyar afuwa ta duniya ta kiyasta cewa kimanin alumar kasar ta Sudan miliyan daya suka rasa rayukan su,sakamakon yaki basasar da ya barke a kasar,yayin kuma alumar ta Sudan miliyan 4.5 suka yi gudun hijira,zuwa wasu kasahe na ketare don tsira da rayukan su.

A lokacin da al-Bashir ya karbi ragamar mulki daga Sadeq al-Mahdi a shekara ta 1989,da sunan ceto kasar Sudan daga hali na kaka na ka yi data sami kanta a ciki,ya sami goyon bayan Hassan al-Turabi shugaban jama’iyar Natinal Islamic Front,kafin kuma daga karshe suka raba gari da juna,a lokacin da al-bashir ya rushe majalisar dokokin Sudan,ya kuma dauki matakai na soke dukanin jama’iyun siyasa dama kafafan yadda labarun Sudan.

Muna fata mai sauraron namu ya gamsu da wanan amsa.