1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin fadar shugaban ƙasar Amurika "White House"

March 11, 2010

Tarihin fadar shugaban ƙasar Amurika "White House" ya samo asuli tun daga shekara 1972

https://p.dw.com/p/MPeC
Fadar shugaban ƙasar Amurika "White House"Hoto: AP

Ku bani tarihin Withe House, wane shugaban Amurika ne ya fara zama  a cikin wannan gida ?

White House kokuma Maison Blanche da farasanci itace fadar shugaban ƙasar Amurika kuma a ciki yake zaune tare da iyalinsa a birnin Washington DC.

An gina wannan hamshaƘen gida cikin shekaru takwas, wato daga 1792 zuwa 1800.

Shuganam ƙasar Amurika na farko ne Georges Washington ya bada kwangilar gina wannan gida.Ƙurraru ta fannin zanen gini guda bakwai suka yi takarar zana  wannan gida mai alforma, to saidai daga ciki, komitin da shugaban ya girka ya gano cewar zanen wani ƙurraren magini mai suna James Hoban ɗan asulin Irland shine ya fi gamsarwa.

An ɗora tubalin tushe na ginin White House ranar 13 ga watan Oktober na shekara ta 1792.

Jimlar kuɗin da aka zuba wurin ginin, a lokacin sun tashi dalla Amurika kimanin dubu 233, to saidai idan aka misalta da darajar Dallar a yanzu an ƙiyasta cewar kuɗin zasu kai kusan dalla miliyan biyu da rabi.

Shugaban ƙasar Amurika na biyu John Adams, shine ya fara zama a cikin White House ranar 1 ga watan Nowemba na shekara ta 1800.

A lokacin da aka gina gidan ana kiran sa kawai fadar shugaban ƙasa. Theodore Roosvelt ne ya fara rubuta  kalmar White House.

Kuma ya fara hakan ne bayan saban farin fentin da akayi wa gidan sakamakon gobarar da yayi  a shekara 1814.Wannan gobara ta faru cikin yaƙin da aka gwabza tsakanin Amurika da Engla, inda dakarun Engla suka kai hari a fadar shugaban ƙasar Amurikan suka kona ta ƙurmus.

Tunda daga shugaban Amurika na biyu John Adams har zuwa shugaba na 44 mai ci yanzu, wato Barack Obama duk wanda ya hau sai gudanar da wata kwaskwarima ga fadar White House , to saidai ya zuwa yanzu kwaskwarima mafi tasiri, itace wadda shugaba Henri Truman yayi, wadda ta ɗauki tsawan shekaru ukku daga 1949 zuwa 1952.Gaba ɗaya aka sabinta ofisoshin a wannan lokaci.

Saidai kuma game da kayan ado da ƙyalliƙyali na cikin gidan, tarihi ya nunar da cewa, matar shugaban ƙasa John Fitzgerald Kennedy ce wanda yayi jagoranci Amurika daga 1961 zuwa 1963 ta ƙayata gidan.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Abdullahi Tanko Balla