Taro a game da rikicin nuklear Korea ta Arewa
October 29, 2007A yau ne ƙasashe 6 masu shiga tsakanin rikicin nuklear Korea ta Arewa, su ka fara shawarwari, a game da tallafin da ya cencenta su baiwa wannan ƙasa a sakamakon haɗin kan da ta bada, wajen yin watsi da mallakar makamin nuklea.
A buda wannan taro agarin PanMunjon dake kaniyaka tsakanin Korea ta Arewa da ta Kudu, tare da halartar dukan ƙasashen da ke da hannu a cikin wannan batu.
A cewar wakilin Korea ta Kudu tuni hukumomin Pyong Yang, sun gabatar da jerin buƙatocin su, a yanzu kawai, ya rage wa mahalrta taron, sunyi nazari, domin tantance hanyoyin biyan wannan bukatoci.
Idan dai ba a manta ba, a watan satumber da ya wuce, a ka cimma yarjjeniya , wada a cikin ta Korea ta Arewa, ta amince da rufe dukan tashoshin ta, na ƙera makaman nuklea, kamin watan desember na wannan shekara.