1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

241110 Südosteuropa Medien

November 24, 2010

Ƙwararrun yankin kudu maso gabashin Turai sun gudanar da taro domin lalubo hanyoyin shawo kan matsalar wariyar jinsi.

https://p.dw.com/p/QHAy
Shugabannin taro akan matsalar wariyar jinsi.Hoto: DW

Ƙwararrun masana a yankin Kudu maso Gabashin Turai sun gudanar da wani taro domin lalubo hanyoyin magance matsalar zazzafan kalamai na nuna wariya da kyamar jinsi da ke addabar ƙasashen wamnan yanki. Halima Balaraba Abbas na da ƙarin bayani....

Ƙwararrun masana da dama a yanki kudu maso gabashin Turai na da ra'ayin cewa kafafe yaɗa labarai su fi mai da hankali ne ga yin ɓaɓatu kan ɓangarori daba-daban na al'uma a maimakon samar da ci gaban rayuwarsu. Dalili kenan da ya sa aka samu ƙaruwar kafafen yaɗa labaru da jam'iyyun siyasa masu kishin ƙasa da ke amfani da su a matsayin hanyar watsa manufofinsu. Liliyana Zurovac shugabar komitin kula da aikin jarida a birnin Sarayevo ta yi kashedi game da abin da ka iya biyo baya inda take cewa:

"A haƙiƙa kalamai na nuna wariya abu ne da ke tattarre da haɗari. Ko shakka babu waɗannan kalamai na yin tasiri sosai akan tunanen al'uma . A saboda haka ne mutane musamman waɗanda ke riƙe da muƙaman shugabanci ke karkata hankulansu ga yin ɓaɓatu game da wani rukuni na jama'a.Muna buƙatar tashi tsaye domin yaƙar wannan ɗabi'a."

To sai dai ba ma a kafafe yaɗa labaru na ƙasashe masu ƙabilu daban- daban irin Bosniya -Herzegovina ne wannan matsala ta yi ƙamari ba. Akwai ƙasashe masu ƙabilu irin ɗaya da ke fama da wannan matsala. Misali a nan ita ce ƙasar Bulgariya, inji Ognan Zlatev shugaban cibiyar samar da ci gaban aikin jarida da ke da mazauninta a Sofia babban birnin ƙasar.

"Yana da ban mamaki cewa a samu matsalar yin kalamai nuna wariyar jinsi a kafafen yada labaru ta kunno kai ne a ƙasar Bulgariya a daidai lokacin da ake samu raguwar wannan ɗabi'a a a ƙasashen kudu maso gabashi Turai. An samu ƙaruwar wannan matsala ne bayan ɓullowar jam'iyyu masu kishin ƙasa a shekarun 2004 da 2005. Waɗannan jam'iyyu suna da jaridun kansu da suke amfani da su wajen yaɗa aƙidarsu ta wariyar jinsi."

Zlatev ya ƙara da cewa waɗannan kalaman dai ana yinsu akan tsiraru 'yan Ƙabilar Roma da ke a wannan ƙasa. To sai dai kuma ba ma akan tsirarun ƙabilu kaɗai wannan matsala ta tsaya ba. 'Yan siyasa su kuma su kan yi wasu kalamai da nufin ɓata sunan abokan hamayyarsu tare da yin amfani da ikonsu na faɗa a ji wajen kaskantar da abokan hamayyar nasu. Hristo Ivanovski editan jaridar Denevic ta ƙasar Macedonia yayi bayani game da haka:

Ya ce "Wannan dai matsala ce da ta kawo rarrabuwar kawuna tsakanin kafafen yaɗa labaru. Kuma shakka babu hakan na banbanta tsakanin kafaen yaɗa labaru masu kishin ƙasa da maciya amanar ƙasa."

Mutane da dama su gano buƙatar shigar da jama'a a cikin muhawarori a matsayin makami mafi inganci wajen yaƙi da wannan ɗabi'a ta nuna kyama ga wani jinsi. Ognan Zlatev ya ba da shawarar ɗaukar matakai guda uku waɗanda a ganinsa za su taimaka wajen yaƙi da wannan ɗabi'a."

Ya ce: "Dabara ɗaya ita ce inganta ƙwarewar 'yan jarida. Akwai kuma buƙatar gindaya sharuɗa ga 'yan jarida waɗanda kowane ɗaya daga cikinsu ke buƙatar biye musu. Sai kuma ƙirkƙrar da hukumar kula da aikin jarida domin tabbatar da inganci a wannan sana'a."

Mawwalafiya: Rayna Breuer/Halima Balaraba Abbas

Edita: Usman Shehu Usman